Likitoci na ne zasu yanke ranar dawowa ta - Buhari

Likitoci na ne zasu yanke ranar dawowa ta - Buhari

- Lai Mohamed, ministan labarai ya jagoranci ziyarar hadiman shugaban kasa zuwa Landan duba lafiyarsa

- Dawowar Shugaban kasa tana hannun likitocinsa

- Buhari ya shafe sama da kwana 90 yana jinya a Landan

Ministan Labarai, Lai Mohamed ya jagoranci ziyarar hadiman shugaban kasa zuwa Landan don duba lafiyarsa.

Tawagar ta hada da jagoran lai Mohamed, Mai basshi Shawara a kan labarai, Garba Shehu, mai magana da yawunsa, Femi Adesina, Hadimar difa’i a yanar gizo, Lauretta Onochie da mai ba da shawara akn harkokin waje, Abike Dabiri.

Hadiman Buhari sun ziyarce shi a Landan

Hadiman Buhari sun ziyarce shi a Landan

Sun gana da shugaban kasa har tsawon sa'a daya da murnar ganin yana samun lafiya. Shugaban kasa yayi murna da ganinsu da yabawa da ayyukan da suke yi a Najeriya.

Tattaunawa akan lafiyarsa da suka yi, Buuhari ya shaida musu dawowarsa tana hannun likitocin sa a yanzu. A cewar shugaban kasa 'Likitoci na ne zasu yanke ranar dawowa ta, domin yanzu su suke bada umarni, nima na koyi bin umarni.' Yana mai kara godewa duk mutanen da suke masa addu'ar samun lafiya.

KU DUBA: Shugabbanin Afrika Suna Zuwa Kasashen Waje Neman Lafiya

Daya daga cikin hadiman ya shaidawa gidan jarida, dawowar Buhari Najeriya tana hannun likitocinsa, don yanzu su suke da ikon da zasu bar shi ya dawo. don haka muna sauraren likitocinsa.

Amma shugaban kasa yana bukatar 'yan Najeriya su cigaba da yi masa addu'a don ya kara samun lafiya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel