Zamu koma gida cikin farin ciki - Lai Mohammaed

Zamu koma gida cikin farin ciki - Lai Mohammaed

-Muna matukar farin ciki yadda muka sami shugaban kasa

-Nayi koyi bin umarnin likitoci yanzu

-Ina bin abubuwan dake faruwa a Najeriya

Minista harkan labarai da al’ada Alhaji Lai Mohammed yace Buhari yana mika gaisuwan sa zuwa ga yan Najeriya lokacin da ya kai mishi ziyara a birnin Ladan tare da tawagar da ta kunshi babban mai magana da yawunsa, Femi Adesina; babban mai bashi shawara akan labarai, Garba Shehu; hadimar difa’I a yanar gizo, Lauretta Onochie. da Abike Dabiri.

Buhari yace zai dawo gida idan likitocin sa sun sallame shi. A jawabin da mai Magana da yawun sa Femi Adesina yayi,yace shugaban kasa yana samun sauki sosai kuma yace “ya koyi bin umarni likitocin sa. Bayan haka ya fito waje da kansa dan ya nuna musu ya samu karfi kuma dauki hotuna tare da su.

Zamu koma gida cikin farin ciki - Lai Mohammaed

Zamu koma gida cikin farin ciki - Lai Mohammaed

“Nayi karfin da zan iya zuwa gida amma likitocin na basu sallame ni ba. Na koyi bin umarnin likitocina saboda su ke dama akaina yanzu."

KU KARANTA:Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

Buhari yace yana bin abubuwan dake faruwa a Najeriya, kuma ya fahimce cewa akwai wasu dake zanga-zangan akan zaman shi a Landan.

Minista harkan Labarai Alhaji Lai Mohammed yace ya ji dadi yanda yaga shugaban kasa yana samun lafiya ya kuma kara da cewa “Yanzu zamu koma gida cikin farin cikin farin ciki. Saboda yadda muka samu shugaban kasa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel