Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai Buhari ya dawo -Charly Boy

Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai Buhari ya dawo -Charly Boy

Shahararren mai bada Nishadi, Charles Oputa(Charly Boy), bai kula da maganar 'yan sanda da suka yi na cewar ya zube kasa a wata zanga-zanga a Abuja don jawo hankalin mutane

Ya shaida wa Sunday Scoop cewa, "Gaskiya ne na fadi. Barkonon tsohuwa ya sa ni jiri kuma na fadi. Na kuma tsaya da maganata cewa wani dan sanda ya buge ni da bindiga. Gwamnatin karya ce kuma haka 'yan sandan ma. Kowa yana cikin hanyar yaudara. Idan mutanen Najeriya sun yarda da gwamnati da 'yan sanda, to, shikenan. Na gaya muku abin da ya faru. Ba aiki na ba ne don yin bayani game da ko mai ya faru. Ina mayar da hankali ga abin da muke yi. Kuskuren da 'yan sanda suka yi shine su fuskanci masu zanga-zangar kamar su (' yan sanda) sun zo domin yaki.

Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai Buhari ya dawo -Charly Boy

Za mu ci gaba da zanga-zanga har sai Buhari ya dawo -Charly Boy

A halin yanzu, ba za su iya fuskantar Boko Haram da 'yan fashi ba. Sun fi so su zalunta talakawa. "

KU KARANTA KUMA:Bugun zuciya ya kama mijin wata mata sanadiyar keta ma sa haddi

Da yake jawabi a kan abin da ya faru a wannan rana mai ban mamaki, ya ce, "Ba su so mu ci gaba da zanga-zangar ba tare da la'akari da gaskiyar cewa mun rubuta musu cewa kai sati biyu ba. Sun amince da zanga-zangar saboda mun yi magana da dukkan jami'an tsaro. A wannan rana, bamuyi wata zanga-zanga ba mun dai samu wurin mun zazzauna ne na 'yan hawowi. A wannan rana, mu bakwai ne kawai muke wurin. Jami'an tsaro sun kasance a gefe kuma ba su so mu fara tara wasu mutane. Don haka sun kunna barkonon tsohuwa, ruwan kwari da kuma karnuka akan mu. Duk da haka, mun ci gaba da zanga-zangar kuma za mu ci gaba. Muna shirin ci gaba da zanga zangar har sai shugaban ya dawo kasar. Idan shugaban ya kasance mahaifina, zan dauke shi daga wannan ofishin kuma in sami magani mai kyau mashi da kuma samar mashi hutu. Amma mun san cewa hannuwansa suna daura . Ba shi ne ke gudanar da ayyukan Nijeriya ba. "In ji shi.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel