Toh fa: Wani tsohon shugaban kasa ya ce ko Allah ma ya amince da PDP

Toh fa: Wani tsohon shugaban kasa ya ce ko Allah ma ya amince da PDP

- Jonathan ya bayyana jam'iyyar PDP a matsayin jam’iyyar siyasa wadda Allah da kansa yake auna

- Tsohon shugaban ya ce jam’iyyar PDP ne mafi girma a jam’iyyun siyasa a Afrika

- Jonathan ya bayyana cewa ya yi imani da PDP, ko Allah ya yi imani da ita

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana jam'iyyar mai adawa ta PDP a matsayin jam’iyyar siyasa wadda Allah da kansa yake auna.

Ya ce ba sabo ba ne don cewa Allah ya amince da tsohon jam'iyyar adawa ba, wanda aka kwatanta da ita a matsayin mafi girma a jam’iyyun siyasa a Afrika.

NAIJ.com ta ruwaito cewa Jonathan ya gabatar da wannan jawabin ne a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta yayin taron jam’iyyar PDP a filin wasa na Eagles da ke birnin tarayya Abuja.

Toh fa: Wani tsohon shugaban kasa ya ce ko Allah ya amince da PDP

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan

Tsohon shugaban ya yi kira ga 'yan Najeriya cewa su ci gaba da tallafawa jam’iyyar da yin addu'a domin nasarar PDP zaben shekarar 2019.

KU KARANTA: Zaben 2019: PDP na yin addu'a dare da rana domin Buhari ya samu lafiya – inji shugaban Jam’iyyar PDP

Jonathan ya ce tare da PDP, babu dan Najeriya da zai ji yunwa.

Jonathan ya ce: "PDP ne kawai jam'iyyar da za ta iya daukaka girman Najeriya. Na yi imani da PDP. Ko Allah ya yi imani da PDP. Tare da PDP ba za ku ji yunwa ba”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel