Zaben 2019: PDP na yin addu'a dare da rana domin Buhari ya samu lafiya – inji shugaban Jam’iyyar PDP

Zaben 2019: PDP na yin addu'a dare da rana domin Buhari ya samu lafiya – inji shugaban Jam’iyyar PDP

- Shugaban jam'iyyar PDP ya ce jam'iyyar za ta ci gaba da yin addu'a domin samu lafiya shugaba Buhari

- Makarfi ya ce burin jam'iyyar ne ganin shugaba Buhari ya samu lafiya kuma ya dawo bakin aikinsa

- Shugaban ya ce jam’iyyar ba za ta saka ido ba, amma za ta yi aiki sosai don lashe zaben 2019

Sanata Ahmed Makarfi, shugaban jam'iyyar mai adawa ta PDP ya ce jam'iyyar za ta ci gaba da yin addu'a domin samu lafiya da kuma dawowar shugaba Muhammadu Buhari.

A wani taron jam’iyyar da aka gudanar a ranar Asabar, 12 ga watan Agusta a Abuja, Makarfi ya ce burin jam'iyyar ne ganin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu lafiya kuma ya dawo bakin aikinsa.

Makarfi ya ce: "Muna wa shugabanmu fatan alheri. Za mu ci gaba da yin addu'a a gare shi, muna son ya samu lafiya domin ya dawo ya ci gaba da jagorancin kasar, amma wannan baya nufin cewa za mu yi sake ko kuma mu zuba ido. Za mu yi aiki sosai don lashe zaben 2019”.

Zaben 2019: PDP na yin addu'a dare da rana domin Buhari ya samu lafiya – inji shugaban Jam’iyyar PDP

Shugaban kasa Muhammadu Buhari

NAIJ.com ta ruwaito cewa sanata Makarfi ya yaba da hukumomin tsaro don tabbatar da cewa an gudanar da taron a cikin wani yanayi mai kariya.

KU KARANTA: Abuja: Tsohon shugaban ‘yan tawayen Neja Delta ya caccaki Charlyboy a kan Buhari

Har ila yau, sanatan ya yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), don nuna rashin bambanci a ayyukan ta.

A cikin jawabinsa, sanata Ben Obi, sakataren kwamitin rikon kwarya na Jam'iyyar PDP, ya ce dole ne ‘yan jam’iyyar su hada hannayensu domin sake mayar da jam'iyyar karagar mulki don ceto Najeriya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel