Ba mu yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa ba - Cewar Gooduck Jonathan

Ba mu yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa ba - Cewar Gooduck Jonathan

-Tsohon mataimakin shuguban kasa Namadi Sanmbo ya halarci taron

-Kuskure ne mutane su rika tunanin cewa inda PDP ke mulki da abubuwa sun fi lalacewa

-Lokacin PDP babu matsalan karanci abinci da hauhawan farashin kayan masarufi

Tsohon shugabankasa Goodluck Jonathan ya bayyana cewa gwamnatin sa bata yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa ba.

Jonathan yace “kuskure ne tunanin da jama’a suke yi na cewa, da shi yaci zaben 2015 da tattalin arzikin kasannan yafi yanzu tabarbarewa.

Jonathan yayi wannan jawabin ne a babban taron da jam’iyyar PDP tayi jiya a Eagles Square dake Abuja.

Ba mu yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa ba-Cewar Gooduck Jonathan

Ba mu yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa ba-Cewar Gooduck Jonathan

A cikin wadanda suka halarci taron hadda tsohon mataimakinsa, Namadi Sambo, tsofaffin gwamnoni da wanda suke kan mulki va yanzu.

KU KARANTA:Kano: Kun san yawan dabbobin da ake kashewa a kowace rana a Kano kuwa

Jonathan yakara da cewa ambaliyan ruwan da akayi lokacin mulkin sa a shekara 2012 shi yakara yanyo wa gwamnatin sa ci baya.

A jawabin sa, “Yace duk da yake yi ba mu kawo karshen cin hanci da rashwa ba amma munyi kokari.

“Naji wasu suna cewa inda ace PDP ke kan mulki yanzu da tattalin arzikin kasan ya fi haka lalace wa. Hakan ba zai taba yiwuwa saboda muna da kwararru a fannin tattalin arzikin kasa."

“Kada mu munata ambaliyan ruwan da aka yi a shekara 2012 shi janyo lalacewan gidaje da gonaki dake kusa da Kogunan Niger da Binuwai."

“Duk da barnan da amabaliyan ruwan yayi, ba a shiga matsalan karanci abinci ba, kuma babu hauhawan farashin kayan masarufi, saboda mun samu nasara wajen inganta noma wanda ya janyo wadatan abinci a kasa."

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel