Kano: Kun san yawan dabbobin da ake kashewa a kowace rana a Kano kuwa?

Kano: Kun san yawan dabbobin da ake kashewa a kowace rana a Kano kuwa?

- Gwamnatin jihar Kano ta ce dabbobi 2,245 ake kashewa a kowace a Kano

- Daraktan ayyukan dabbobi ya ce daga cikin adadin 420 ne shanu da 1,750 tumaki da kuma 75 rakumi

- Darektan ya kuma bayyana damuwa kan rashin isashen likitoci masu duba dabbobin

Gwamnatin jihar Kano ta ce akalla dabbobi 2,245 ake kashewa a kowace rana a wasu abattoirs 4 da ke garin Kano domin al’umma.

Dokta Shehu Bawa, daraktan ayyukan dabbobi a ma'aikatar aikin gona da ma'adanai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Kano ranar Asabar, 12 ga watan Agusta cewa daga cikin adadin, 420 ne shanu.

Bawa ya ce 1,750 na dabbobin sun kasance tumaki da awaki, kuma 75 sun kasance raƙuma ne.

Kano: Kun san yawan dabbobin da ake kashewa a kowace rana a Kano kuwa?
Ana kashe kimani dabbobi 2,245 a kowace rana a Kano

Bawa ya ce abattoirs inda aka yanka dabbobin sun hada da wanda ke Bachirawa a karamar hukumar Ungoggo da Unguwa Uku a yankin karamar hukumar Tarauni da kuma wanda ke Tudun Wada a yankin karamar hukumar Nasarawa.

KU KARANTA: Ya kamata Shugaba Buhari ya bar mulki Inji Limamin coci

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Bawa ya kuma bayyana damuwa kan rashin yawan likitocin dabbobi da suka kamata su gano lafiyar dabbobin kafin a yanka su.

Darektan ya bukaci gwamnatin jihar da ta yi karin likitocin kula da dabbobi da sauran ma'aikata don tabbatar cewa an duba dabbobin da ake kashewa da kuma tsabtace nama a abattoirs kafin a kai su kasuwanni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel