Sakon Kirista: Obasanjo yace a saurari dawowar Yesu Almasihu kwanan nan

Sakon Kirista: Obasanjo yace a saurari dawowar Yesu Almasihu kwanan nan

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a ranar Asabar yace kirista su zauna cikin shirri domin Yesu Almasihu ya kusa dawowa kuma duniyar ma ta kusa zuwa karshe

Obasanjo ya fadi wannan maganar ne a cocin Apostolic Faith a lokacin wani taro da ake kira Camp meeting Concert a fikin taron camp ground da ke Igbesa a jihar Ogun.

A cewarsa, yana so ya tafi aljanna domin yayi ta yin wakokin yabon Ubangiji tare da mala’iku.

Sakon Kirista: Obasanjo yace a saurari dawowar Yesu Almasihu kwanan nan

Sakon Kirista: Obasanjo yace a saurari dawowar Yesu Almasihu kwanan nan

Ya kamata kowa ya kasance cikin shirri domin zuwan Yesu Almasihu, babu wani tantama a cikin lamarin.

“Ina da wani aboki da yace min idan an je Aljanna, wakokin yabon Ubangiji za’ayi tayi har sai an gaji, kuma hakan yayi kama da rayuwar kurkuku.

DUBA WANNAN: Rasuwar wata mata a Zamfara ya tada kura a jihar

Amma yadda naga yan Kwaya na rera wakokin yabo yau, ni kam ina son in tafi aljanna domin in hadu da mala’iku muyi ta wakokin yabon tare.

“Yesu Almasihu yazo wannan duniyan ne domin ya cece mu kuma yayi mana bushara da rayuwa ta har abada, muna da abin alfahari da tinkaho,” Inji shi.

Obasanjo ya cigaba da cewa Ubangiji bai gyara Najeriya ba saboda yan Najeriya basu rungumi Ubangiji ba a rayuwarsu.

Muna da matsaloli da yawa dake adaban kasan nan, idan zamu yi ma kanmu adalci.

“Nigeria zata gyaru idan muka koma ga Ubangiji, Abin da zamuyi wajen gyara kasan nan yana hannun mu.

Sifiritenda Apostolic Faith na shiyar Arewa ta yamma, Reveran Adebayo Adeniran yace hakuri da juna, zaman lafiya da zama tare ne kawai zai kawo cigaba mai dorewa a Najeriya.

Yace, dole ne mu hada hannu baki daya domin gina kasar mu tare da kaunan juna, adalci, da kuma yafe wa juna.

Daga karshe yayi kira da kiristan Najeriya da suyi ma shugabanin su addu’a domin samun cigaba a kasar mu Najeriya.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha duka da cizo a hannun wata mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel