Abuja: Tsohon shugaban ‘yan tawayen Neja Delta ya caccaki Charlyboy a kan Buhari

Abuja: Tsohon shugaban ‘yan tawayen Neja Delta ya caccaki Charlyboy a kan Buhari

- Tsohon shugaban ‘yan tawayen yankin Neja Delta ya kalubalanci Charlyboy a kan shugaba Muhammadu Buhari

- Dokubo ya yi Allah wadai da zanga-zangar cewa shugaba Buhari ya dawo ko ya yi murabus

- Dokubo ya ce tsohon minista na man fetur da albarkatun kasa ba ta kula da ‘yan kabilar Ijaw komai ba a lokacin da take minista

Tsohon shugaban ‘yan tawayen yankin Neja Delta, Alhaji Mujahid Asari Dokubo ya yi tir da shaharerren mawakin nan Charlyboy a kan jagorancin wani zanga-zangar lumana a kan shugaba Muhammadu Buhari inda suka bukaci shugaban ya dawo bakin aikinsa ko ya yi murabus.

Da yake jawabi a wani bidiyon a shafinsa ta Facebook, Dokubo ya yi Allah wadai da Charlyboy na rashin goyon bayan fafutukar kafa yankin Biyafara kuma ya yi masa ba'a.

Dokubo ya ce jami’an tsaro sun fesa masa borkonun tsohuwa inda ya suma.

Abuja: Tsohon shugaban ‘yan Tawaye Neja Delta ya caccaki Charlyboy a kan Buhari

Tsohon shugaban ‘yan tawayen yankin Neja Delta, Alhaji Mujahid Asari

NAIJ.com ta tattaro cewa, Dokubo ya kuma kira tsohon minista na man fetur da albarkatun kasa, Diezani Alison-Madueke a matsayin "wauta" domin ba ta kula wa ‘yan kabilar Ijaw komai ba a lokacin da take minista.

KU KARANTA: EFCC: Idan ‘yan Najeriya sun san yawan kudin da aka sata daga kasar za su gigice – inji Shugaban EFCC

Ya ce wadanda minitan ke hurda da su a lokacin da take ofis duk sun yi watsi da ita yanzu ganin halin da take ciki.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel