'Dodo' ne ya ce na yanke 'mazakuta' na

'Dodo' ne ya ce na yanke 'mazakuta' na

Wani mutum a jihar Ondo ya rede mazakutan sa da reza kuma ya ce 'dodo' ne ya sanya shi aikata hakan

Wani abun al'ajabi ya faru a yankin Obanla na garin Akure dake jihar Ondo, inda wani mai matsakaitan shekaru, Oluwole Aiyeloja ya yanke mazakutan da reza a bainar jama'a.

Oluwale ya sake yunkurin yanke marainan sa, inda a kayi sa'a wasu nagari su kayi azamar hana shi sannan su ka kwace rezar daga hannun sa kuma suka mika rahoto ofishin 'yan sanda na kurkusa domin a garzaya da shi asibiti.

Wata me sayar da katin waya da abin ya faru a gabanta, Olaolu Oluyede, ta bayyana mamakin faruwar wannan abu da Oluwole ya aikata.

'Dodo' ne ya ce na yanke 'mazakuta' na

'Dodo' ne ya ce na yanke 'mazakuta' na

Ta ce, "ina cikin sana'ata ta siyar da katin waya inda wani ya tabo ni ya gwada min abinda ke faruwa a kan wani benci da ke kusa da mu"

"Mutane sun razana da cewar mutum mai shiga ta kamala kawai ya fara kwale wandon sa a bainar jama'a, sannan kuma ya aikatawa kan sa wannan abu. Wannan abin firgici ne don yadda jina ya ke zuba."

Inda ta cigaba da bayani ko ya na da cikakken hankali, ta ce, ya dai yi shiga ta kamala.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Kakakin 'yan sanda na jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar da faruwar wannan abu, kuma ya ce ana gudunar da bincike don suna tunanin Oluwole ya na da tabin hankali ko kuma shafar aljannu.

Ya ce, "mun tambayi Oluwole, ya ce wai 'dodo' ne ya sanya shi yanke mazakutan sa don wani sa'in ya na masa maganganu a kunnensa, kuma shi ya sa ya aikata hakan. Kuma dodo ya sanya shi ya yanke marainan sa ma"

Joseph ya ce, "ba za mu tuhumi Oluwole da aikata wani laifi ba duk da ya illata kan sa domin ba kisan kan sa ya yi yunkuri ba wanda wannan shine laifi ne a wajen mu."

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA

An zargi Abba Kyari a kan ajiyar biliyan 50 na NNPC a bankuna wanda ta sabawa tsarin asusun TSA
NAIJ.com
Mailfire view pixel