Ya kashe kan sa da 'ya'yan sa 2 saboda matar sa ta kama gabanta

Ya kashe kan sa da 'ya'yan sa 2 saboda matar sa ta kama gabanta

Rashin tawakkali ya sanya wani mutum kisan 'ya'yan sa biyu da kashe kan sa saboda sun rabu da uwar gidan sa

Wani mutum mazauni kuma dan asalin kasar Afirka ta kudu, Njabulo Khomohas, na kauyen Mophela, ya kashe kananun 'ya'yan sa biyu sannan shima ya kashe kan sa.

Jaridar DAILY SUN ta ruwaito cewa, dama tuni ya ke ta ikirarin zai kashe kan sa saboda uwar gidan sa ta kama gabanta, wanda 'yan uwan sa su ka bari baki ya hakura.

A ranar larabar da ta gabata ne aka gano gawar 'ya'yan na sa, Njabulo mai shekaru 2 da Sibenelo mai shekaru 3, a rataye da igiya a cikin wani gidan haya.

Ya kashe kan sa da 'ya'yan sa 2 saboda matar sa ta kama gabanta

Ya kashe kan sa da 'ya'yan sa 2 saboda matar sa ta kama gabanta

Wata 'yar uwa ga marigayin, Sindi Mzulwini, ta bayyana cewa, ya dauki yaran ne a wajenta don daman a wajenta suke zama, inda ya shirga ma ta karyar zai kai su wajen likitan gargajiya ne. Ta ce babban abinda yafi kona ma ta rai shine rashin tausayin da ya nuna a kan yaran.

Sindi ta ce, "mun yi magana da shi ba sau daya ba akan ya rungumi kaddarar rabuwa da matar sa. inda ya nuna mu su kamar ya hakura kuma ya dauki shawara"

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

'"Ya'yan sa ba su da alaka da rikin da yake tsakanin su da mahaifiyar su, duda cewa basu ji dadin rashin sa amma da sai ya fi a ce kan sa kadai ya kashe ya bar yaran."

"Ya ma ni karyar cewa waje likitan gargajiya zai kai su, amma da mu ka ji abinda ya karu kashe gari sai mu ka san cewa ashe tuntuni ya kulla tuggu a cikin taku."

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato

Gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta tallafawa mata 100 da kyautar kudi a Sakkwato
NAIJ.com
Mailfire view pixel