EFCC: Idan ‘yan Najeriya sun san yawan kudin da aka sata daga kasar za su gigice – inji Shugaban EFCC

EFCC: Idan ‘yan Najeriya sun san yawan kudin da aka sata daga kasar za su gigice – inji Shugaban EFCC

- Shugaban hukumar EFCC ya ce idan ‘yan Najeriya sun san adadin dukiyar da aka sata a kasar za su yi mamaki

- Shugaban ya ce mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa na iya kokarinsu don kawo wa hukumar tikas a ayyukan ta

- Magu ya ce hukumar na bin dukkan hanyoyin da za a mayar da wasu barayin gwamnati dags kasashen ketare zuwa Najeriya

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu ya bayyana cewa dukiya da kadarorin da barayin gwamnati masu fashi da baro suka sata daga kasar wanda hukumar ta kwace har zuwa yanzu wani kalilan ne kawai bisa ga wanda suka sata.

Shugaban ya kara da cewa akwai dukiya da dama wanda aka boye a wasu wurare a kasar da kuma a sassa daban-daban na duniya, ya ci gaba da cewa ‘yan Najeriya ba su ga wani abu ba tukuna.

Kamar yadda NAIJ.com ke da labari, Magu ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan talabijin na Channels a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta, Magu ya ce zai tabbatar cewa ya dawo da duk kudaden da beraye masu yi wa kasar zagon kasa suka sata.

EFCC: Idan ‘yan Najeriya sun san yawan kudin da aka sata daga kasar za su gigice – inji Shugaban EFCC

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu

Wadannan mutane na iya kokarinsu don kawo muna tikas a ayyukan hukumar, amma muna kokarinmu”. A cewar Magu'

KU KARANTA: Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

“Ba hukumar ta mu kawai ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan ba, saboda haka ina so in yi kira ga sauran hukumomin gwamnati masu yaki da cin hanci da rashawa don ƙara kokarin da kuma taimaka mana ganinmun yaki da cin hanci da rashawa”.

“Muna bi duk kudaden da aka dawo da su kuma mun yi niyyar dawo da su duka kuma zamu hukunta duk wadanda aka samu da laifi”.

“Muna da sane cewa wasu daga cikinsu suna kasashen waje kuma muna bin dukkan hanyoyin da za a mayar da su zuwa kasar". In ji Magu

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel