Sultan na Sakkwato ya yabi Tony Elumelu akan samar da aikin yi ga 'yan Arewa

Sultan na Sakkwato ya yabi Tony Elumelu akan samar da aikin yi ga 'yan Arewa

Sarkin musulmi ya jinjinawa shugaban kungiyar bankin UBA akan gudunmawar da cibiyar sa ta ke bayarwa a Arewacin Najeriya

Sarkin musulmi, Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku, ya yabawa cibiyar Tony Elumelu wanda Tony Elumelu din ya kafa, game da gudunmawar da ta ke bayarwa ga harkokin kasuwancin da kuma samar da ayyuka ga matasa a Arewa.

Sultan ya ba da yabo a yayin da shugaban kungiyar bankin UBA da kuma shugaban cibiyar Tony Elumelu Foundation ya ziyarci sarkin, ba da dadewa ba kafin zaman tattaunawa akan tattalin arziki na jami'ar Usman Danfodiyo dake Sokoto, inda Elumelu ya ba da jawabi ga daliban jami'ar da shugabannin da ke cikin gari.

Sultan ya bayyana cewa, taka rawar Elumelu, ta hanyar kafa tushe, da kuma tallafin kasuwancin ya samar da ayyuka kuma ya taimaka wajen samar da tsaro a Arewa ta hanyar samarwa matasa masu yawo a hanyoyi da tituna abin yi.

Sultan na Sakkwato ya yabi Tony Elumelu akan samar da aikin yi ga 'yan Arewa

Sultan na Sakkwato ya yabi Tony Elumelu akan samar da aikin yi ga 'yan Arewa

"Muna bukatar karin ire-iren Tony Elumelu. Muna bukatar karin ire-iren su Aliko Dangotes. Muna ci gaba da godiya game da abin da kuke yi wa matasanmu saboda lokacin da kuka dauke wadannan yara daga tituna, kuna samar da hanyar da za su iya rayuwa cikin sauki kuma wannan al'amari ya na rage faruwar laifuka da bayar da tsaro,"inji shi.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

A cikin jawabin Elumelu, "ya yabawa jami'ar don ba shi damar bayyana sakonninsa ga dalibai. Ya kuma umarci daliban da suyi amfani da karatunsu, ta yadda zai taimaka musu su fahimci matsayinsu don ciyar rayuwar Afrika gaba."

"Yan kasuwa kawai na iya haifar da miliyoyin ayyukan da muke bukata don kare tattalin arzikin mu daga talauci."

Ya kuma umurce su da su dauki alhakin bunkasa nahiyar Afirka, ya na cewa: "Babu wanda zai iya bunkasa Afirka sai mu. Makomar Afrika ta kasance a hannun dukanmu 'yan Afrika."

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel