'Shugabanni kansu suke hallakawa idan suka wawushe asusun gwamnati'

'Shugabanni kansu suke hallakawa idan suka wawushe asusun gwamnati'

Wani shugaba a jihar Imo ya ce masu wawushe kudaden gwamnati kansu kawai suke hallakawa

Shugaban cibiyar Eziama Bond akan aminci ta kungiyar garin Eziama Osuh-Ama a yankin Isiama Mbano na jihar Imo ya ce ma su rike asusun gwamnati su na halaka kansu ne a yayin da suka sace kudaden da ake bukata don kyautatawa al'ummarsu.

Ya ce rashin yin aiki na gari cikin ofisoshin su zai iya jingina ga cin hanci da rashawa ga jama'a, girman kai, rashin sani ciwon kai na abinda ya kamace su, da sauransu.

Da yake jawabin na sa a yayin bikin rantsar da shi a matsayin shugaban kungiyar, Unogu ya ce, "Abin da ya kashe duk wani ma'aikacin gwamnati shi ne karkata akalar kudade da suka biyo ta hanayarsu wanda na jama'a ne. Sai su manta da cewar cin kudin al'umma ba dadi bane amma halaka a garesu."

'Shugabanni kansu suke hallakawa idan suka wawushe asusun gwamnati'

'Shugabanni kansu suke hallakawa idan suka wawushe asusun gwamnati'

Unogu, wanda shine Manajan Global Lifting Services Ltd., ya alwashin cewa gwamnatinsa za ta kasance mai gaskiya da rikon amanar al'amura kuma zai sadaukar da kan sa don aiwatar da ayyukan ci gaba a cikin al'umma.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Unogu ya umarci shugabannin kungiyar da su tsaya akan daidai a duk abin da suka sa a gaba, yana cewa babban burinsa shi ne inganta harkokin al'ummar fiye da yadda ya same ta.

Ya kara da cewa, aikin wucin gadi na shekaru uku zai isa ya aiwatar da shirye-shiryensa. Ya ce shugabancinsa zai tsara shirye-shirye game da harkar lafiya da hanyar kawo kwanciyar hankula, da ayyukan aikin gona da kuma samar da wuraren nishadi da wasannin yara.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel