Zaben shugaban kasa na Kenya ya zo da tarnaki, har an kashe mutum 11, hakan na kama da Najeriya?

Zaben shugaban kasa na Kenya ya zo da tarnaki, har an kashe mutum 11, hakan na kama da Najeriya?

- Sharhin zabe a Kenya ya duba yadda sakamakon zaben shugaban kasa a kasar Kenya ya kawo kashe kashe a shekarun baya da kuma na bana, shin me yasa a Afirka ake kashe-0kashe kawai saboda zabe?

Anyi zaben shugaban kasa a kasar Kenya dake gabashin Afirka, tsakanin abokan takara biyu da sun dade suna hamayya a kasar, wadda ta rabu bisa doron kabilanci da bangaranci.

Zaben shugaban kasa na Kenya ya zo da tarnaki, har an kashe mutum 11, hakan na kama da Najeriya?

Zaben shugaban kasa na Kenya ya zo da tarnaki, har an kashe mutum 11, hakan na kama da Najeriya?

Zaben na ranar Talata ya ayyana shugaba mai ci Uhuru Kenyatta, dan tsohon shugaban kasar na arko, ya kayar da abokin hamayya Raila Odinga wanda tsohon Fira Ministansa ne.

Sai dai fadin sakamakon zaben a jiya, ya jawo kufular magoya bayan Raila Odinga fita tituna domin nuna fushinsu. Shi kuma Odinga ya ki karbar kaye cikin ruwan sanyi, inda yace jam'iyya mai mulki ce tayi masa magudi.

A baya ma dai an sami irin wannan kazamin rikici wanda ya kashe mutane dubbai a shekarar 2007, saboda kawai kaye da Raila Odinga yasha, bayan kamfe na kabilanci da ya ratsa kabilun kasar daga kowanne bangare.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019 inji fadar shugaban kasa

Masu sanya ido dai daga kasashen duniya sun ce zaben sahihi ne, ciki kuwa harda tsohon ministan harkokin wajen Amurka John Kerry.'

Yanzu haka dai har 'yan sanda sun bindige mutum 11 saboda wai sun tada zaune tsaye a gari.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Atiku ya shawarci gwamnatin Najeriya a kan abinda ya kamata ta yi don dakatar da masu yin hijira daga kasar

Atiku ya shawarci gwamnatin Najeriya a kan abinda ya kamata ta yi don dakatar da masu yin hijira daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel