Babu wanda zai kara kukan yunwa idan mu ka karbi mulki - Jam'iyyar PDP

Babu wanda zai kara kukan yunwa idan mu ka karbi mulki - Jam'iyyar PDP

- PDP tace babu wanda zai kara kukan yunwa zuwa 2019

- Jam'iyyar tace mulkin APC ya jefa jama'a cikin wahala

- Sen. Ahmad Makarfi ya sha alwashin tika APC da kasa

Jam'iyyar adawa PDP tace mulkin APC ya jefa jama'ar Kasar cikin kangi. PDP tace babu wanda zai kara kukan yunwa zuwa 2019.

Babu wanda zai kara kukan yunwa idan mu ka karbi mulki - Jam'iyyar PDP

Shugaban kwamitin rikon-kwarya na PDP

Shugaban kwamitin rikon-kwarya na PDP Sanata Ahmad Makarfi ya sha alwashin tika APC da kasa a zabe mai zuwa na 2019. Shugaban na PDP yace za su yi bakin kokarin su wajen ganin sun doke APC sun dawo mulki don da haka aka san Jam'iyyar.

KU KARANTA: Manyan Yan PDP sun isa wurin taro

Babu wanda zai kara kukan yunwa idan mu ka karbi mulki - Jam'iyyar PDP

Taron Jam'iyyar PDP a yau

Makarfi yace idan Jam'iyyar ta dawo mulki za ta kawo tsari na raba bashi ga matasa domin su kafa kan su. Hakan zai kauda yunwa kuma ya rage talauci har ta kai 'Yan kasar su ji su cikin kudi. PDP ta zargi Jam'iyyar APC mai mulki da jefa mutane cikin wahala.

Yayin da zaben 2019 yake ta matsowa kusa ana ta kokarin gano bakin zaren siyasar kasar. Hakan ya sa Jam’iyyar PDP ta kira wani babban taro a yau dinnan. Ana kokarin zaben masu fitar da gwanin dan takara a Jam’iyyar adawar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Matan jam'iyyar adawa ta PDP

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel