Gangamin PDP: Jonathan ya ci taro a Abuja

Gangamin PDP: Jonathan ya ci taro a Abuja

- Ana kokarin zaben masu fitar da dan takara a PDP

- Manyan ‘Yan PDP sun cika Abuja a yau dinnan

- Tsohon shugaban kasa Jonathan shi ma ya isa taron

Yayin da zaben 2019 yake ta matsowa kusa ana ta kokarin gano bakin zaren siyasar kasar. Hakan ya sa Jam’iyyar PDP ta kira wani babban taro a yau dinnan. Ana kokarin zaben masu fitar da gwanin dan takara a Jam’iyyar adawar.

Gangamin PDP: Jonathan ya ci taro a Abuja

Jonathan ya ci taro a Abuja

A taron na PDP dai tsohon Shugaban kasar wata Dr Goodluck Ebele Jonathan ne ya ci taro a Abuja. Dr. Jonathan ya isa filin dazu a mota inda dubban magoya baya su kayi masa lale maraba da zuwa.

KU KARANTA: APC na cikin rikici a Jihohi

Gangamin PDP: Jonathan ya ci taro a Abuja

Taron PDP a Abuja yanzu haka da manya a zaune

Mu na nan dai mu na kawo maku rahotanni da bayanai kai tsaye inda Jam'iyyar adawa ta PDP ta fara taron gangamin ta na farko bayan kotun koli ta raba gardama tsakanin Ali Sherrif da Sanata Ahmed Makarfi.

Kawo yanzu matsaloli na cigaba da bullowa a cikin Jam'iyyar APC mai mulki bayan da aka tsige manyan Jam'iyyar na Jihar Bayelsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Jawabin matan jam'iyyar PDP a taron gangamin kwanaki

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel