Hukumar DSS ta cafke mutum 18 ma su aikata miyagun laifi

Hukumar DSS ta cafke mutum 18 ma su aikata miyagun laifi

Hukumar binciken miyagun laifuka ta kasa, (Deparment of State Service, DSS) ta bayyana cewa ta cafke mutane 18 da ake zargin su da aikata laifin garkuwa da mutane da ya yi kamari a cikin kasar nan

A wani rahoton jami'in hukumar, Tony Opuiyo, ya bayyana cewa a ranar 3 ga watan Yuli ne a unguwar Kakuri ta jihar Kaduna su ka cafke; Haliru hassan, Usman Abdulkadir, Yusuf Saidu, Abubakar Suleiman, Uzairu Bawa da Sani Abubakar.

Opuiyo ya ce, a ranar 4 ga watan Yuli, sun cafke wasu mutum biyu, Rabiu Sani (Dogo) da Abubakar Sani, su ma da su ka shahara da garkuwa da mutane a kan hanyar Zariya zuwa Funtuwa dake karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.

Hukumar DSS ta cafke mutum 18 ma su aikata miyagun laifi

Hukumar DSS ta cafke mutum 18 ma su aikata miyagun laifi

Jami'in ya ce, Sani ya shahara da yin garkuwa da mutane kuma shi ne babban mai samar da makamai ga ma su aikata miyagun laifi na jihohin Kaduna, Kano, Taraba da Jos.

Ya ce an cafke su ne tare da wata shudiyar mota kirar Volkswagen mai lamba MGU 106 EA, karamar bindiga daya, Ak-47 hudu, manyan bindigu guda biyar , kudi sama da Naira 400, 000 da makamantansu.

A ranar 5 ga watan Yuli, hukumar ta su ta cafke wasu mutum biyu da su ke garkuwa da mutane a titin Ikara dake karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano, wadanda su na cikin kungiyar shahararrun ma su garkuwa da mutane na dajin Falgore a jihar Kano.

KU KARANTA KUMA: Amfanin ruwan kokwamba guda 5 a jikin dan Adam

Jami'in ya cigaba da kawo ire-iren masu aikata laifin garkuwa da mutane da hukumar ta su ta yi nasarar cafkewa da sanadinsu na mutane biyar daga birnin tarayya da kuma biyu a jihar Kogi

A kan harkokin kunar bakin wake na Boko haram kuma,a ranar 1 ga watan Yuli, sun cafke Usman Musa, Isa Halidu, Ibrahim Dauda, Bature Mohammed, Buhari Dauda, Inusa Usman da Adamu Ibrahim a unguwar Sakwai ta karamar hukumar Kachiya dake jihar Kaduna.

Da wannan ne hukumar ta ke kara godiya da kara karfin gwiwa akan taimakon da ke bayarwa al'umma wajen cafke dukkannin wa su ma su aikata laifi don samar da zaman lafiya a kasa baki daya.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel