Yanzu-Yanzu: Manyan jiragen ruwa 2 makare da kaya sun kama da wuta a garin Fatakwal

Yanzu-Yanzu: Manyan jiragen ruwa 2 makare da kaya sun kama da wuta a garin Fatakwal

Labaran da muke samu da zafi-zafin su yanzu suna nuni ne da cewa wasu manyan jiragen ruwa guda biyu makare da kayayyakin masarufi sun kama da wuta a gabar ruwan garin Fatakwal dake can jihar Ribas a kudancin kasar nan.

Mun samu labarin dai cewar jiragen ruwan da suka kama da wutar a ranar juma'a watau jiya kenan da safe har yanzu ba'a tantance ainahin musabbabin gobarar ba amma dai an tabbatar da cewa daya daga ciki yana dauke ne da man fetur.

Yanzu-Yanzu: Manyan jiragen ruwa 2 makare da kaya sun kama da wuta a garin Fatakwal

Yanzu-Yanzu: Manyan jiragen ruwa 2 makare da kaya sun kama da wuta a garin Fatakwal

NAIJ.com kuma har ila yau ta samu karin haske daga wata majiyar ta mu inda tace dakyar ne masu aikin kashe gobarar suka iya shawo kan gobarar.

A cewar majiyar: "Banda Allah ya taimaka an tari lamarin da wuri, da tayi barna sosai don kuwa ba'a san iya asarar dunbin dukiyar da za'a yi ba a wurin."

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel