Yan shi'a suji tsoron Allah su dena yi wa Buhari mugunyar addu'a - Gudaji Kazaure

Yan shi'a suji tsoron Allah su dena yi wa Buhari mugunyar addu'a - Gudaji Kazaure

Dan majalisar wakillan nan kuma shahararren mai goyon bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari dake wakiltar mazabar kananan hukumonin Kazaure, Yankwashi, Gwiwa da kuma Roni duka a cikin jihar Jigawa Honarable Muhammad Gudaji Kazaure ya kira yan shi'a da su tsagaita yi wa shugaba Buhari mugunyar addu'a hakanan.

Majiyar mu dai ta ruwaito mana cewa dan majalisar yayi wannan kiran ne a yayin da yake wata fira a gidan rediyo mai matsakaicin zango na Dala kai tsaye a jihar Kano.

Yan shi'a suji tsoron Allah su dena yi wa Buhari mugunyar addu'a - Gudaji Kazaure

Yan shi'a suji tsoron Allah su dena yi wa Buhari mugunyar addu'a - Gudaji Kazaure

NAIJ.com ta samu kuma cewa dan majalisar a cikin firar ya nanata cewa shugaba Buhari har yanzu bai dawo gida ba ne ba a dalilin mugayen addu'oi da kuma asirrai da wasu al'ummar Najeriya suke yi masa ba dare ba rana.

Dan majalisar daga nan ne kuma sai ya roki mabiya mazhabar ta Shi'a da su ji tsoron Allah su dena yi masa munanan addu'oin don kuwa ba laifin sa bane ba kisan da ssojojin kasar suka yi wa wasu daga cikin su a watannin baya.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

An ɗaura ma wata budurwa auren dole, Angon ta ya yaba ma aya zaki bayan sati 3 kacal

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel