Bincike kan dalilin da yasa ake zuwa asibitoci a kasashen ketare

Bincike kan dalilin da yasa ake zuwa asibitoci a kasashen ketare

- Shugabanni daga kasashen Afrika suna zuwa kasashen waje neman magani

- Rashin amincewa da asibitocin kasar su ke sa su zuwa wasu kasashen neman lafiya

- Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari har yanzu yana jinya a Ingila

Bincike kan dalilin da yasa Shugabannin Afrika suke zuwa kasashen waje neman magani. Musamman shugabannin Najeriya, Zimbabwe, Benin da Angola. Rashin yadda da tsarin kiwon lafiyar asibitocin kasarsu ne yake hana su fita kasashen waje.

Shugabannin da dama basu wadata asibitocin kasar da kayan aiki, hakan yana hana munatar kasar samun wadataciyyar lafiya.

Bincike kan dalilin da yasa ake zuwa asibitoci a kasashen ketare
Bincike kan dalilin da yasa ake zuwa asibitoci a kasashen ketare

Shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe mai shekara 72, ya ziyarci asibiti a kasar Singapore na uku kenan a shekarar nan da ta kama.

Asibitocin Najeriya na fama da rashin wadataccen kudi wajen samar da magani. Tun watan Mayu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yake jinya a Landan, ya kwashe tsawon kwana sama da 90 ba ya kasar.

A watan Mayu ne Jose Eduardo dos Santos, shugaban kasar Angola na tsawon shekara 38, ya je Spaniya duba lafiyarsa.

DUBI WANNAN: Obasanjo ya ce Yeriman Bakura yayi shari'a ne saboda tsoron kamu

Amma wasu shugabannin sun kwatanta zuwan ba wai a matsayin sun fi samun cikakkiyar kulawa a asibitin kasar waje ba.

Amma in dai har shugabannin zasu cigaba da fita kasashen waje asibiti neman lafiya, ba lallai su inganta na kasarsu ba.

Babban abin da ya kamata su duba shine wadatar da kudi da magunguna don a samun lafiya. Domin kudin da shugabannin suke kashewa a asibitin kasashen waje zai iya isa a wadata na kasar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel