Kun ji ranar da kotu ta saka don sauraren karar Sanata Dino Melaye da INEC?

Kun ji ranar da kotu ta saka don sauraren karar Sanata Dino Melaye da INEC?

Wata kotun tarayya dake zama a babban birnin tarayya Abuja ta saka ranar 11 ga wata mai kamawa na Satumba a matsayin ranar da ta kebe domin sauraron karar da Sanata Dino Melaye ya shigar game da kiranyen da jama'ar mazabar sa ke son yi masa.

Babban alkalin kotun mai saurar karar mai suna Nnamdi Dimgba ne bayyana hakan ga manema labarai bayan da ya gama sauraron lauyoyin wanda ake kara da masu karar da suka tafka muhawara kan lamarin.

Kun ji ranar da kotu ta saka don sauraren karar Sanata Dino Melaye da INEC?

Kun ji ranar da kotu ta saka don sauraren karar Sanata Dino Melaye da INEC?

NAIJ.com dai samu cewa a kwanan bayanan ne dai Sanata Dino Melaye ya shigar da kara a kotun inda yake kalubalantar sanya hannun wasu matattu daga cikin mutanen da suka sanya hannun amincewa da kiranyen.

Kafin nan kuma tun farko dai al'ummar da Sanatan ke wakilta dai suka yi wani yunkurin cire wakilin nasu a majalisar dattijai bayan da suka bayyana cewa su basu gamsu da wakilcin da yake yi mau ba.

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel