Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

- Gwamnatin Buhari ta ci zabe ne bisa doron yaki da satar kudin talakawa

- Majalisa ta ce lallai baza ta tabbatar da Magu a kujerar EFCC ba

- An kama kudade da yawa a hannun jami'an tsohuwar gwamnati

Shugaban hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC), Ibrahim Magu, a ganawar sa da gidan jaridar DAILY TRUST yayi bayani mai tsawo a kan batutuwa da suka shafi aikin sa na yaki da cin hanci da karya tattalin arzikin a mataki daban - daban.

Magu, yace yana aikin sa ne ba don ya burge ko ya ci mutunci wani ba, sai don yin hakan shine abinda ya dace, kuma domin hakan ne a Ka bashi wannan aiki. "Zan ci gaba da yin aiki na ko da ba wanda zai yaba min makutar dai a kan gaskiya nake" a fadin magu.

Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

Magu ya koka, ya ce barayin dukiyar kasa na kai masa farmaki ta ko'ina

Magu, ya ce "na rike gaskiya don haka nake cikin kwanciyar hankali, ina yin bacci na har da minshari ba tare da wata fargaba ba duk kuwa da matsin lamba da takura da nake fuskanta ta hanyoyi masu yawa".

Da yake amsa tambayar ko rashin tabbatar da shi daga yan majalisar dattawa na katsalandan da aikin nasa, Magu ya ce "ko kadan hakan bai shafi aiki na ba, ina da cikakken iko na yin aiki na". Da aka tamabaye shi shin ko me yasa yan majalisar suka ki tabbatar da Kai? Magu ya amsa da cewa "sanin wannan amsa, aiki ne naku na yan jarida, kune ya kamata ku binciko dalilin su, ba nine zan fada maku ba".

Magu, ya Kara da cewa yaki da cin hanci da ta'annaci abu ne da ya shafi duk yan kasa, sannan yayi kira ga duk yan Nigeria dasu bawa hukumar goyon baya domin murkushe wannan mummunar dabi'a.

Magu, yace ya samu ganawa da hukumar jami'o'i ta kasa domin domin neman hadin kan hukumar wajen yakar cin hanci dake cikin jami'o'in mu na kasar nan sannan da kiran su kirkiri wani darasi da zai koyar da daliban jami'o'i illolin cin hanci da hanyoyin yaki da shi.

Dan gane da surutan da wasu ke yi na cewar ba'a hukunta wadanda aka samu da aikata laifin cin hanci ko ta'annata dukiyar al'umma, Magu, ya ce "shi yasa nake son kowa ya shigo cikin yakar cin hanci da rashawa, saboda alhaki ne da ya rataya wuyan kowa, kuma muna kokari wajen fadakarwa da ilimintar da mutane a kan yadda tun a farko ma zamu hana sata domin samun saukin wahalar bincike da gurfanar da wadanda su ke wawure arzikin kasa". Magu ya Kara da cewa "Ni aiki na ya tsaya ne kawai a bincike da gurfanar da masu barnar gaban Kotu bisa ga shaidu da sakamakon binciken mu. Akwai lauyoyin mu da su kare duk shaida da sakamako da muka gabatar saidai masu laifin na dauko manyan lauyoyi masu shaidar SAN domin su tabbatar sun kawo tsaiko wajen yi masu hukunci, a wasu lokuta ma da irin wadannan manyan lauyoyi suke amfani wajen mika cin hanci ga alkalai.

Magu yace babban tsaiko ga yaki da cin hancin shine yadda shi ma yaki da cin hancin ke yakar yakin da ake yi da shi ta kowanne bangare. Masu wawure kudin jama'a na bibiyata da matsin lamaba a gare ni duk inda bake.

A kan tsarin fallashe da hukumar ta fito da shi, Magu yace, tsarin yana basu matsala domin a mafi yawan lokaci idan suka irin wannan bayanai na sirri suna zuwa basu samu abinda suka zo nema ba, daga bisani kuma kaga ana masu dariya. Yace suna taka tsan - tsan da duk wani bayani na sirri kafin suyi aiki da shi.

DUBI WANNAN: Yadda Yerima ya kusa ruguje Najeriya saboda tsoron Ali Gusau

Dangane da dawo da kudade da aka sace aka boye kasashen waje, Magu ya ce a yanzu suna samun cigaba wajen kokarin dawowa da Nigeria su, sabanin kalubalen da suke samu a baya. Ya ce yanzu akwai tsaye - tsare tsakanin hukumar da wasu kasashe da suka hada da Dubai da USA wajen dawowa da Nigeria kudaden da aka boye a kasashen.

Magu ya bayyana niyyar hukumar sa na mallakar sansani na kashin kanta domin bawa ma'aikatan ta hotoro domin yanzu haka da sansanin bada horon sojin Nigeria dake Kaduna suke amfani duk da hakan ba yana nuni da cewar suna bawa ma'aikatan su horon sojoji ba ne.

Magu yace yana aiki tukuru, ba dare ba rana, amma duk da haka ya kan ware lokacin hutu da na motsa jiki.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel