Kaico! Iyali sun kashe kansu saboda matsin tattalin arziki

Kaico! Iyali sun kashe kansu saboda matsin tattalin arziki

Wani magidanci mai shekaru 47 tare da matarsa mai shekaru 44 sun kashe Kansu a cikin dakin su, ta hanyar shan guba.

Al'amarin ya faru ne ranar alhamis a Uran kamar yadda jaridar Hindustan ta kasar India ta wallafa.

Ma'auratan sun bar takarda a dakin da suka mutu dauke da rubutun cewar sun yanke shawarar su kashe kansu ne saboda tsananin talauci da tarin rigingimu kudi dake addabar su.

Kaico! Iyali sun kashe kansu saboda matsin tattalin arziki

Kaico! Iyali sun kashe kansu saboda matsin tattalin arziki

An gano gawarwakin Yusuf Adam da matar sa Fatima ne bayan makwabtan su sun kula da cewar basu fito tsakar gida ba tsawon kwana guda. Bayan an balle kofar dakin nasu ne a ka samu gawar su a dakin nasu sannan gefe guda ga wata kwalbar guba da ake zargi ita suka sha suka mutu kamar yadda jami'in yansandan yankin, Majge, ya fada.

Marigayi yusuf, kamar yadda yake kunshe cikin takardar da a ka samu a dakin na su, yace ya ranci kudi masu yawa wasu watanni da suka wuce, kudin da yace ba zai iya biya ba. A takardar dai bai bayyana adadin kudin ba.

DUBI WANNAN: Dalilin da yasa ba'a yi wa dimokuradiyya juyin mulki ba tun 1999, inji Obasanjo

Yansanda sun ayyana mutuwar tasu a matsayin mutuwa ta hanyar hadari.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel