Zaben Jam'iyya APC yana ta barin baya da kura

Zaben Jam'iyya APC yana ta barin baya da kura

- Zaben APC na Jihohi ba ya haifar da 'da mai ido

- Kusan rudani ake ta samu a duk inda aka yi zaben

- Wannan abu dai na iya raba kan 'ya 'yan Jam'iyyar

Yayin da zaben 2019 yake ta karasowa ka iya cewa zaben APC na Jihohi da aka yi tayi na ta barin baya da kura.

Zaben Jam'iyya APC yana ta barin baya da kura

Jam'iyyar APC na cikin rudani

A Jihar Kaduna dai abin bai yi dadi ba. Sanatocin APC da wasu da su ka bangare sun kai kara har wurin Shugaba Jam'iyya su ka jawo hankali cewa a guji irin kura-kuren PDP. Sai dai wannan bai hana uwar Jam'iyya ta amince da zaben da aka yi ba.

KU KARANTA: Wasu 'Yan Majalisa ba su tabuka komai

Zaben Jam'iyya APC yana ta barin baya da kura

'Yan Jam'iyyar APC wajen kamfe

A can Jihar Kano ma dai haka abin yake inda aka zabi Shugaba amma har yanzu dai kamar akwai ta cewa game da zaben. A Jihar Kogi kuwa an nemi a kawo hatsaniya ma dai lokacin da za ayi zaben. A irin su Jihar Katsina dai da alamu ba a samu matsala irin haka ba.

Kawo yanzu matsaloli na cigaba da bullowa a cikin Jam'iyyar APC mai mulki bayan da aka tsige manyan Jam'iyyar na Jihar Bayelsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi wa Gwamnatin APC zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel