Jami'o'i na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayya

Jami'o'i na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayya

- Wasu Jami'o'in Najeriya ba su bi umarnin Gwamnati ba

- An haramtawa Jami'o'i yin kwas din Diploma na cikin gida

- Haka kuma an nemi a dakatar da jarrabawa PUTME

Bincike na musamman da NAIJ Hausa tayi ya nuna cewa Jami'o'i da dama na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayya.

Jami'o'i na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayya

Jami'ar Legas ta Najeriya

Ba sabon labari bane cewa Hukumar NUC ta haramtawa Jami'o'in Gwamnatin Tarayya yin kwas din difloma na cikin gida da su ka saba. Manyan Jami'o'i irin Ahmadu Bello ta Zariya kwanan nan ma su ka fara shirin saida fam na wannan difloma na bana.

KU KARANTA: Malamai na shirin shiga yajin aiki

Jami'o'i na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayya

Jami'aar ABU na cigaba da yin difloma

Haka kuma ma'aikatar ilmi ta nemi a dakatar da jarrabawar nan ta PUTME da ake yi bayan an rubuta UTME ta shiga Jamia'a. Ko a bara dai irin su Jami'ar Bayero ta Kano tayi wannan jarrabawa sa sunan gwaji duk da an hana.

Kwanaki Jami'ar Ahmadu Bello ce ta 1 a Najeriya kaf yayin da a cikin Jami'o'in da ba na Gwamnati ba Covenant University ke gaba. A cikin Jami'o'in Jihohi kuwa babu irin ta Legas Inji Hukumar NUC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An kama masu laifi a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel