Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a Jami'o'in Najeriya

Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a Jami'o'in Najeriya

- Kungiyar ASUU na shirin shiga wani dogon yajin aiki

- Da dama na Malaman sun zabi a tafi dogon yajin aiki

- Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a wajen masu karatu

Mu na samun kishin-kishin din cewa Kungiyar ASUU ta Malaman Jami’a na shirin shiga wani dogon yajin aiki.

Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a Jami'o'in Najeriya

Yajin aiki ya kawo dar-dar a Jami'a

Kamar yadda mu ka samu labari da dama na Malaman Jami'a sun zabi a tafi yajin aikin da sai inna ta gani saboda rashin jituwa tsakanin su da Gwamnati. Shirin yajin aiki ya kawo dar-dar a wajen masu karatu a halin yanzu.

KU KARANTA: Gwamnati ta taimakawa 'Yan Borno

A wasu Jami'o'in irin su Usman Danfodio ta Sokoto da Ahmadu Bello ta Zariya an fara jarrabawa a halin yanzu. Wannan dai ya raba kan daliban da ke karatu. Wasu sun ce aikin yayi masu yawa dama can hutu su ke nema, wasu kuma na maza su gama.

An haramtawa Jami'o'i yin kwas din Diploma na cikin gida an kuma nemi a dakatar da jarrabawa PUTME. Sai dai bincike na musamman da NAIJ Hausa tayi ya nuna cewa Jami'o'i da dama na cigaba da sabawa Gwamnatin Tarayyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ana yi wa Gwamnati zanga-zanga

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel