Jerin wasu 'Yan Majalisan Katsina da ba su da kudiri ko daya tun hawan su

Jerin wasu 'Yan Majalisan Katsina da ba su da kudiri ko daya tun hawan su

- Mun kuma kawo wasu 'Yan Majalisan Tarayya da ba su da kudiri

- Watau tun hawan su kujerar ba su gabatar da kudiri ko guda ba

- A baya mun kawo jerin wasu 'Yan Majalisan da ba su tabuka komai

Idan ba ku manta ba, a baya mun kawo jerin 'Yan Majalisan Jihar Kano da ba su tabuka komai kamar yadda Jaridar Daily Trust tayi nazari.

Jerin wasu 'Yan Majalisan Katsina da ba su da kudiri ko daya tun hawan su

'Yan Majalisan Najeriya a zama

Yanzu haka mun koma kan 'Yan Majalisar da ke Wakiltar mazabun Jihar Katsina wanda bincike ya nuna cewa tun da aka rantsar da su shekaru 2 da su ka wuce har yau babu wani kudiri da su ka gabatar a gaban Majalisar ko guda.

KU KARANTA: Abin da ya hana sojoji juyin mulki

Wadannan ‘Yan Majalisun su ne Honarabul Sani Fago, Kabir Shuaibu, Danlami Kurfi, Ahmed Dayyabu Safana, Murtala Isa, Ibrahim Murtala, Amiru Tukur, Muntari Dandutse, Suleiman Salisu, Babangida Ibrahim da Mansir Ali Mashi.

A irin su Jihar Jigawa dai akwai wasu ‘Ya Majalisa 11 a wannan sahu irin su Adamu Mohammed, Magaji Aliyu Da’u, Abubakar Hassan Fulata, Yuguda Hassan Kila, Rabiu Garba Kaugama, Usman Ibrahim Auyo, Mohammed Gudaji Kazaure, Mohammed Gausu Boyi da Ibrahim Abdullahi Dutse.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An damke wani mai laifi a Legas

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel