Wani manomi ya shiga hannu da laifin kisan barawon gonar sa

Wani manomi ya shiga hannu da laifin kisan barawon gonar sa

Wani manomi, Moses Erutaya ya shiga hannun hukuma da laifin daukar doka a hannun sa na kashe wani barawon gonarsa ma suna Jonathan da ya saci curin filanten guda 35

Manomin na jihar Edo ya amsa laifin kashe Jonathan inda ya bayyana cewa marigayin ya dade ya na masa sata a gonar sa tun 2007.

Ga kalamansa, " Na fara noma a wannan gonar a shekarar 1998. A shekarar 2007 kuma ina tsimayin filanten dina ya nuna, wani ya shiga gonar ta wa ya sace curika 60 na filanten. Na yi korafin wannan abu amma aka ce ai ko babu wanda zai min gadi a gonar tawa. Tun a wannan lokacin ne na fara lura da sa ido akan gonar da kaina."

Wani manomi ya shiga hannu da laifin kisan barawon gonar sa

Wani manomi ya shiga hannu da laifin kisan barawon gonar sa

"Jonathan ya taki rashin sa'a a shekarar 2017 inda ya yi satar curi 35. Na bishi har wurin da zai siyar na tuhumce shi, sai kuwa ya ce ai curi 7 kawai ya sata a gona ta. Na tasa shi sai munje ya nuna ma ni inda ya sato sauran filanten din."

KU KARANTA KUMA: Wani mutum mai shekaru 45 ya yi wa yaro mai shekaru 9 fyaden da ya zama ajalinsa

"Jonathan ya taki rashin sa'a a shekarar 2017 inda ya yi satar curi 35. Na bishi har wurin da zai siyar na tuhumce shi, sai kuwa ya ce ai curi 7 kawai ya sata a gona ta. Na tasa shi sai munje ya nuna ma ni inda ya sato sauran filanten din."A

" A kan hanyar mu ne ya tsaya. Ya kafe keken sa da wani katoka, kawai sai na yakito katakon na buga ma sa a kai, inda nan ya fadi wanwar matacce. 'Yan uwansa sun zo wuri na neman sa sai na ce musu ai ya kama gabansa daga bisani kuma na kai su har kan gawar sa."

"Ina rokon gwamnati da ta yafe ma ni."

Kwamshinan 'yan sanda na jihar, Haliru Gwandu, wanda ya tabbatar da faruwar haka ya ce nan ba da jimawa ba za su mika Moses gaban alkali.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar

Abin da ya kamata gwamnatin Najeriya ta yi don dakatar da masu kaura daga kasar
NAIJ.com
Mailfire view pixel