Tsawon shekaru 65 wata 'yar shekara 33 za ta yi a gidan kaso saboda kisan 'yar ta ta hanyar dilmiyar a ruwa

Tsawon shekaru 65 wata 'yar shekara 33 za ta yi a gidan kaso saboda kisan 'yar ta ta hanyar dilmiyar a ruwa

Rashin tausayi ya sanya waya mata ta kashe 'yar ta kuma ta boye gawar har na tsawon watanni 16 inda kotu ta yanke ma ta daurin shekara 65 a gidan kaso

Kotu ta jefa wata uwa , Keishanna Thomas mai shekaru 33, a gidan kaso na tsawon shekaru 65 da laifin kisan 'yar ta mai shekaru 11 wanda kuma ta boye gawar na tsawon watanni 16 a cikin firinji.

Jaridar UK SUN ta ruwaito cewa, duk da rashin amincewa da zargi da kuma tuhumar da ake yi wa wannan mata, wata kotu a birnin Florida dake kasar Amurka, ta yanke wa wannan mata mai shekaru 33 hukuncin zama a gidan kaso na tsawon shekara 65 da laifin kisan kai da kuma cin zarafin karamar yarinya da kuma zaluntar gawar 'yar.

Rahotannin sun bayyana cewa, an gano daskararriyar gawar Janiya Thomas, mai shekaru 11, a watan Oktobar 2015, a cikin wani firinji da mahaifiyarta ta rufe da kwado kuma ta kaiwa gidan danginta dake Bradenton.

Tsawon shekaru 65 wata 'yar shekara 33 za ta yi a gidan kaso saboda kisan 'yar ta ta hanyar dilmiyar a ruwa

Tsawon shekaru 65 wata 'yar shekara 33 za ta yi a gidan kaso saboda kisan 'yar ta ta hanyar dilmiyar a ruwa

Samun labarin bacewar Janiya ne, ya sanya dangin na ta bude wannan firinji ta karfi, inda suka gano gawar a cikin kankara.

KU KARANTA KUMA: Mahaifiyar wata 'yar shekara 12 ta shiga hannun hukuma da laifin mayar da 'yar ta karuwar haya

Masu binciken kwa-kwaf akan gawar mutum, sun binciko cewa, kafar Janiya ta dama ta karye na tsawon makonni kafin mutuwar ta kuma ta mutu ne sanadiyar rashin abinci da dilmiyarwa a cikin ruwa.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Canji! Gwamnatin shugaba Buhari zata sake ɗiban sabbin hafsoshin Yansanda
NAIJ.com
Mailfire view pixel