'Naira 10,000 na sayi zuciyar dan Adam domin na yi sihiri'

'Naira 10,000 na sayi zuciyar dan Adam domin na yi sihiri'

Wani mutum da ake tuhuma da laifin mallakin zuciyar dan Adam ya bayyana yadda ya samu wannan zuciya ta hanyar saye a wajen abokin sa

A ranar Alhamis ta 10 ga watan Agusta, 'yan sandan jihar Ogun su ka cafke wani mutum mai suna Bakare Olalekan akan laifin mallakar zuciyar dan Adam.

A yayin da manema labari su ka tattauna da Olalekan, ya bayyana mu su cewa, ya saye wannan zuciyar ne a wurin abokin shi, wanda ya bayar da sunan shi da Oye, akan kudi Naira 10,000 da nufin amfani da wannan sassa na jkin dan Adam wajen aikata sihiri na neman sa'a.

A cewar sa, " daga bisani shi Oye ya sayar min da zuciyar mutum guda uku kuma ya yi amfani da daya wajen yin sihiri wanda daga baya kuma na siyar da ragowar biyun ga wani shima dake tsare a tare da Olalekan."

'Naira 10, 000 na sayi zuciyar danAdam domin na yi sihiri'

'Naira 10, 000 na sayi zuciyar danAdam domin na yi sihiri'

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmed Illiyasu, wanda ya gabatar da wanda ake tuhuma a gaban manema labarai, ya ce binciken da' yan sanda suka yi ya nuna cewa Olalekan na daga cikin kungiyar mutane hudu da suka kashe wata yarinya mai shekaru 16, Olayinka Adebayo, a watan Agustan shekarar bara.

KU KARANTA KUMA: Annobar wata cuta ta kashe mutane sama da 70 a jihar Kwara

Kwamishinan 'yan sandan ya ce nan ba da jimawa ba, za su tura mutumin da ake tuhuma kotu domin gurfana a gaban alkali.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.naij.com

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure

Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
NAIJ.com
Mailfire view pixel