Dalilin da ya sa Nnamdi Kanu ke kira ga raba Najeriya Inji wani babban Malami

Dalilin da ya sa Nnamdi Kanu ke kira ga raba Najeriya Inji wani babban Malami

Bishof Abraham Udeh, babban sakataren Mount Zion Faith Global Liberation Ministries Nnewi, masu ayyukan ceto na duniya a Nnewi, Anambra ya ce ya goyi bayan kira ga raba gardama na kasa

- Bishof Udeh ya ce kiran Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar 'yan asalin na Biafra (IPOB) ya cancanta

- Amma duk da haka ya yi kira ga dukkan 'yan Najeriya su tashi don tallafawa a gudanar da raba gardama

Bishof Abraham Udeh, babban sakataren Mount Zion Faith Global Liberation na ayyukan Gida da Duniya a Nnewi, Jihar Anambra ya bayyana dalilin da yasa Nnamdi Kanu,mai jagoran 'yan asalin Biafra (IPOB) ke kira ga raba gardama.

Wani sanannen Bishop na Krista ya bayyana dalilin da ya sa Nnamdi Kanu ke kira ga raba gardamar kasa

Wani sanannen Bishop na Krista ya bayyana dalilin da ya sa Nnamdi Kanu ke kira ga raba gardamar kasa

A cewar Vanguard, Udeh ya ce kiran da Kanu ya ke yi na raba gardama daidai ne, amma abin takaici ne cewa wasu suna sukar shi.

Ranar Laraba, 9 ga Agusta, a cocinsa, ya ce, Kanu ya yi kira ga kauracewar zabe, sai dai idan an gudanar da raba gardaman kasa.

KU KARANTA KUMA:Yadda Yariman Bakura na Zamfara ya kusa ruguza Najeriya - Cif Obasanjo

NAIJ.com ya ruwaito cewa, ya ce kiran da ake yi na sake gyara bata lokaci ne,saboda babu abin da zai sa Gwamnatin tarayya na APC ta amince da shi.

Ya ce: "Wadannan dalilai ne suka sa na ba da goyon bayan kashi 100 ga kundin raba gardama da Kanu ya kaddamar da ita.kuma ina da hujjar cewa da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari yana sauraro ne, to da mutanen da suke buƙatar sake gina Najeriya ba zasu bukaci haka ba. "'

Babban malamin mai kula da ayyukan kiyaye zaman lafiya ta duniya na Mount Zion ya ce dukkan 'yan Najeriya su tashi da goyon baya ga zaben raba gardama.

A halin yanzu, NAIJ.com ya bayar da rahoton cewa Majalisar Dattawan Arewa a ranar Laraba 9 ga watan Agusta ta yi zanga-zangar neman bukatar kama Nnamdi Kanu akan hadin kan Najeriya.

Kungiyar da suka shiga tituna a karkashin 'yan sanda sun ce hadin kai na kasar ba ta da wata matsala yayin da yake kira ga kama Nnamdi Kanu,mai jagoran' yan asalin Biafra.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim

Taurin kai: Rahma Sadau ta yi fatali da korar da akayi mata, ta shirya sabon fim
NAIJ.com
Mailfire view pixel