Biyafara: Ka nizanci jihohin Neja Delta ko kuma.., karanta – Inji tsagerun ‘yan Neja Delta ga Nnamdi Kanu

Biyafara: Ka nizanci jihohin Neja Delta ko kuma.., karanta – Inji tsagerun ‘yan Neja Delta ga Nnamdi Kanu

- Tsagerun ‘yan Niger Delta sun gargadi shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya nizanci jihohin Neja Delta

- Kungiyar ta ce ta shiga gwagwarmaya domin samu zaman lafiya a yankin da Najeriya

- NDV ta gargadi kamfanonin mai na kasashen waje dake aiki a yankin cewa su komar da hedkwatarsu zuwa yankin

Tsagerun ‘yan Niger Delta a karkashin kungiyar Niger Delta Volunteers, NDV sun gargadi kungiyar 'yan asalin Biyafara, IPOB masu fafutukar kafa yankin Biyafara da su nizanci jihar Akwa Ibom.

Suka ce "ba mu cikin ɓangare na ‘yan Biyafara; muna cikin yankin Niger Delta ne”.

'Yan Neja Delta sun bayar da gargadin ne yayin da suka yi ikirarin cewa shugaban kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu cewa yankunan Neja Delta na Biyafara ne.

Biyafara: Ka nizanci jihohin Neja Delta ko kuma.., karanta – Inji tsageru ‘yan Neja Delta ga Nnamdi Kanu
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, shugaban NDV, Janar Ekpo Ekpo ya ba da sanarwar yayin da yake jawabi da 'yan jarida a Uyo, babban birnin jihar Akwa Ibom.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram sun kashe masunta 34 a jihar Borno

Ekpo ya ce, kungiyar NDV ta shiga cikin gwagwarmaya domin samu zaman lafiya a yankin da Najeriya.

Ekpo ya kuma gargadi kamfanonin mai na kasashen waje dake aiki a yankin cewa su komar da hedkwatarsu zuwa yankin Neja Delta kafin watan Oktoba 1.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel