Rahoton Forbes na bana: Duba ko na nawa Dangote yazo cikin masu kudin duniya 10 bakaken fata

Rahoton Forbes na bana: Duba ko na nawa Dangote yazo cikin masu kudin duniya 10 bakaken fata

- Aliko Dangote dai dan asalin jihar Kano ne wanda ya shiga kasuwanci tun yana yaro

- Mike Adenuga shi ya biyo Dangote na biyu a Najeriya

- Jaridar Forbes dai ita ce babbar jarida ta lissafta masu kudin duniya

Jaridar gulma ta Forbes da ke Turai, ta fidda sabon rahoton ta na bana, inda ta lissaffta arzikin masu kudin duniya wadanda suka tara sama da dala biliyan daya, cikin su 2,043.

Bakaken fata goma sun yi fice, ciki ko harda naku Aliko Dangote, wanda aka saka dukiyarsa kan zabbar dala har biliyan sha uku. Naira Tiriliyan 5 kenan, kusan kasafin kudin Najeriya na bana.

'Yan Najeria mutum uku na daga cikin sahun bakar fata mutum goma masu kudin duniya wadanda yawan su yakai mutum 2,043.

A duk bakaken fata masu kudi na Duniya, Dangote da Adenuga sun yi zarra inji jaridar Forbes
A duk bakaken fata masu kudi na Duniya, Dangote da Adenuga sun yi zarra inji jaridar Forbes

Yanzu dai Bakar fata mutum goma ne a cikin masu kudin na duniya sabanin su goma sha biyu da aka bayyana a shekarar data gabata.

Aliko Dangote, Mike Adenuga, da Folorunsho Alakija sun mallaki kudi da adadinsu yakai biliyoyin dalar amurka.

Yanzu haka Aliko Dangote shine bakar fata da yafi kowa kudi da adadin dalar amurka 12.2 ($12.2billion), yayinda mike Adenuga ke biye dashi a mataki na uku da adadin dalar amurka 6.1 ($6.1billion), sai kuma Folorunsho Alakija a mataki na takwas da adadin kudi biliyan 1.61($1.61billion).

A gida Najeria, Aliko Dangote shine yafi kowa kudi yayinda Mike Adenuga ke biye dashi a mataki na biyu.

KU KARANTA KUMA: Tir! Waka ta cin mutuncin kabilar Ibo ta cika gari

A lissafi dai kwatankwacin dukiyar Aliko Dangote shine abinda kasa Najeriya, yan siyasar ta da talakawanta, mahandamanta da 'yan kishinta kan dogara da shi a shekara daya, mu miliyan 200. Kasafin bana Tiriliyan shida na naira, kadara da dukiyar Dangote, Tiriliyan 5 na naira.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a email dinmu na labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel