Addu'o'i: Wani Gwamnan Kudu ya biya Limaman Musulunci makudan kudi

Addu'o'i: Wani Gwamnan Kudu ya biya Limaman Musulunci makudan kudi

- Gwamna Ben Ayade ya sakawa Limamai da alheri

- Gwamnan ya rabawa Malamai kudo Naira Miliyan 10

- Limaman sun yi wa Ben Ayade addu'ar samun nasara

Mun ji labarin cewa Gwamnan Jihar Kuros-Riba Farfesa Ben Ayade ya sakawa Limaman Jihar sa da irin alherin da su kayi masa.

Addu'o'i: Wani Gwamnan Kudu ya biya Limaman Musulunci makudan kudi
Gwamnan Jihar Kuros-Riba Farfesa Ben Ayade

Gwamna Ben Ayade ya cika alkawarin sa da yayi wa Malaman Addinin Musulunci a Jihar inda ya ba su kudi Naira Miliyan 10 a dalilin addu'o'in da aka rika yi masa lokacin yana yakin neman zabe da kuma neman nasara a Kotu bara.

KU KARANTA: Buhari ya gana da Obasanjo

Addu'o'i: Wani Gwamnan Kudu ya biya Limaman Musulunci makudan kudi
Gwamna Ayade da Shugaban kasa

Shugaban Malaman Jihar Kabir Saad Ibrahim ya bayyanawa Jaridar Daily Trust wannan yace Gwannan bai yi kasa a gwiwa ba kuma za su cigaba da yi wa Gwamna Ben Ayade da Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu'a tare da kokarin hada kan Jama'a.

Kwanaki Gwamnan Jihar Kuros Riba Ben Ayade yace shi da mutanen Jihar sa sun dage ba dare ba rana wajen yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a ya samu lafiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Da wani abu Shugaba Buhari zai karya a Ofis?

Asali: Legit.ng

Online view pixel