Boko-Haram suna ma garuruwan dake kusa da Maiduguri Barazana - Mazauna

Boko-Haram suna ma garuruwan dake kusa da Maiduguri Barazana - Mazauna

-Ba ma iya barci a cikin dare

-Akwai alamun sashen Albarnawi sun fara daukan hanyan Shekau

-Na yi imani idan gwamnati tayi abun da ya kamata za a sako ma,aikatan da aka sace

Yan kungiyan Boko-haram suna tsare-tsaren yadda zasu kai wa garin Maiduguri farmaki, ajiya wsu mazaunan garuruwan da ke makwabtaka da garin suka fada haka.

Amma mazaunan da suke zama a kauyukan dake kusa da Maiduguri sun gaya wa Daily Trust ajiya cewa,akwai bukutar sa ido da kula saboda yan ta’adan sun kusan shiga birinin Maiduguri.

Wasu kafofi da basa son a ambaci sunayen su, sun ce yan boko haram suna zuwa kauyen su tsoratar da su kuma suna zuwa ne tare da yan mata yan kuna bakin wake.

Boko-Haram suna ma garuruwan dake kusa da Maiduguri Barazana-Mazauna
Boko-Haram suna ma garuruwan dake kusa da Maiduguri Barazana-Mazauna

Yan ta'adda suna mana barazanar kawo ma kauyen mu hari idan muka yi magana: daya daga cikin yan kauyen ya fada mana haka.

KU KARANTA:Fusattatun matasa sun far ma Shehu Sani da Hunkuyi a

Ya jero sunayen garuruwan da ke kusa da Maiduguri wanda ke fuskantar barazanar yan kungiya.ya kunshi Dunomari, Ngubodori, Garin Maliki, Jiddari, Tamsugamdu, Garin Kwayam, Zaragajri da Jelta Kawu dake kewaye da Jami’an Maiduguri.

Wata majiya ta ce al'ummomin dake kusa da hanya barikin suma suna fuskanta barazana yan ta'adda. " da wurare kamar Bale, Galtimari, Fasha, Garin Shuwa, Kayamla, Taujeri da Kayamari suna kasa yin barci daddare dan tsoro,"

Abun mamaki ne ganin yadda yan kungiyan suka kashe sojoji da ma’aikatan hako mai da mallaman jami’an Maiduguri.

Bangaren Abum Musa’ab Albarnawy,Dan Mohammad Yusuf, tsohon shugaban kungiyan da aka kashe, ya fito da wani bidiyo da ya nuna ma’aikatan jami’an Maiduguri da suka sace, Dr .Solomon Yusuf yana kira da gwamnatin Najeriya ta biya duk bukatun kungiyan dan ceton rayuwan su..

“Ba a san bangaren Albarnawy da kasha-kashe ko yin awon gaba da mutane ba, hakan shine dalilin da yasa suka raba jaha da Shekau.nayi imani idan gwamnati suka yi abun da yakamata za a sako ma’aikatan hako man da aka sace da ran su. Nasan harin da kungiyan ta kai a ranar talata tayi ne dan tura wa gwammnati sako, da kuma samun kudi wajen karban ma’aikatan jami’an Maiduguri,” ya ce.

A bisa dukan alamu sashen Albarnawy sun fara daukan hanyan Shekau wanda ya samu abun da yakeso da gwamnati akan yan matan Chibok,” Inji wani Captain mai ritaya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel