Hako mai: Mutanen Maiduguri sun yi tir da Gwamnatin Tarayya

Hako mai: Mutanen Maiduguri sun yi tir da Gwamnatin Tarayya

- Wasu ‘Yan Borno sun ce kul aka dakata da aikin hako fetur

- Wasu ma na cewa akwai dai makarkashiya tun ba yau ba

- Jama’an su ka ce a dakatar da ta’addanci ba hako fetur ba

Mun samu labari cewa wasu mutanen Maiduguri sun ce ba su yarda a daina hako man fetur ba. Mutanen Yankin su kace ayi maganin Boko Haram ba a daina hako fetur ba.

Hako mai: Mutanen Maiduguri sun yi tir da Gwamnatin Tarayya
Hoton masu aikin hako mai a Maiduguri

Matakin da aka dauka na tsaida aikin hako mai a Arewacin Najeriyar ya jawo babatu a bakin wasu mutanen Maiduguri. Mun fahimci cewa jama'a da dama a kafafen yada labarai na zamani sun ce ba su yarda a daina hako fetur ba da sunan rikicin Boko Haram.

KU KARANTU: Sultan zai shawo kan Inyamurai da Yan Arewa

Hako mai: Mutanen Maiduguri sun yi tir da Gwamnatin Tarayya
Malaman Maiduguri da aka tsare

Wasu dai na ganin akwai makarkashiya don kuwa an dade ana neman wanda zai hako fetur a Yankin na kasar. Ministan fetur Ibe Kachikwu yace ba za a cigaba da aikin hako mai a Kasar ba har sai an Inganta harkar tsaro.

Yanzu haka wasu na tunani 'Yan Boko Haram sun dawo Jihar Borno da karfin su don kuwa barnar da aka yi kwanan nan har a cikin Garin Maiduguri. Jiya dai Ministan ilmi ya kai ziyara Maiduguri inda aka ce ba za a rufe Jami'ar ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Yadda mota ta kashe wani dan siyasa a Legas

Asali: Legit.ng

Online view pixel