Wa'adi: Sarkin Tsafe ya riga mu gidan gaskiya

Wa'adi: Sarkin Tsafe ya riga mu gidan gaskiya

- Dukkan mai rai aka ce mamaci ne

- Allah ya yiwa sarkin Tsafe rasuwa na jihar Zamfara

Rahotanni daga kwamishinan kananan hukomi na jihar Zamfara, Alhaji Muttaka Rini ya bayyana cewa, Allah ya karbi ran sarkin Tsafe wanda wasu kan ce 'Yan doton Tsafe, Alhaji Habibu Aliyu.

Sarkin ya rasu ne a babban asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo a jihar Sokoto bayan da ya dan yi jiya ta wata 'yar gajeruwar rashin lafiya, kuma ya rasu ya bar mata 4, 'ya'ya 25 da jikoki 62.

Marigayi Alhaji Habibu ya gaji sarautar Tsafe ne daga wajen mahaifinsa marigayi Alhaji Aliyu 'Yan doto a shekarar 1991. Za a yi jana'izar sa a fadar garin Tsafe da misalin karfe 2:00 na rana.

Gwamnan jihar kum ciyaman na kungiyar gwamnonin Najeriya, Alhaji Abdulaziz Abubakar yari, bayyana damuwarsa akan wannan rashi.

KU KARANTA: Gurbatattun 'yan siyasa su na amfani da Boko Haram

Mai magana da yawun gwamnan, mai bashi shawara akan harkokin ganawa da jama'a, Alhaji Ibrahim Dosara, ya bayyana cewa, wannan babban rashi ne ba ga iyalai, 'yan uwa, da masarautar jihar Zamfara kadai ba, amma rashi ne ga gaba daya jama'ar Najeriya..

Yace marigayi sarkin ya bar wani babban gurbi wanda zai wahala a samu wanda zai maye, duba da irn yadda yake gudanar da al'amuransa, tsayuwa kan gaskiya, da jarumta a tsawon mulkin na shi na masarautar Tsafe.

Kuma da wannan ne gwamnan yake yiwa iyalen 'Yandoto, masarauta da jama'ar Tsafe da kuma masarautar jihar Zamfara baki daya.

Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na sada zumunta a:

https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel