Boko Haram: An gabatar da mayankan Boko Haram 43 da suka mika wuya zuwa sansanin sake tarbiyar da su a Gombe

Boko Haram: An gabatar da mayankan Boko Haram 43 da suka mika wuya zuwa sansanin sake tarbiyar da su a Gombe

- An gabatar da ‘yan Boko Haram da suka mika wuya ga Operation Safe corridor don sake tarbiyar da su

- Attahiru ya ba da tabbaci cewa za a ba maharan sabon rayuwa ta hanyar sake tarbiyar da su

- Kwamandan ya bukaci muharan da su rungumi shirin da zuciya daya

Mayakan ‘yan kungiyar Boko Haram 43 da suka mika wuya ga dakarun Operation Lafiya Dole makonni da suka gabata sun kasance a jirgin sama na hukumar sojin sama na Najeriya zuwa Gombe a ranar Asabar, 22 ga watan Yuli inda za a hada su da sauran mayakan kungiyar da suka mika wuya don sake tarbiyar da su.

Da yake jawabi yayin da yake gabatar da mayakan da suka mika wura ga Operation Safe corridor, babban kwamandan Operation Lafiya Dole, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ba da tabbaci cewa za a ba maharan wani sabon rayuwa ta hanyar sake tarbiyar da su.

Kwamandan ya bukaci muharan da su rungumi shirin da zuciya daya don zai taimaka musu kuma za su amfana da ita.

Boko Haram: An gabatar da mayankan Boko Haram 43 da suka mika wuya zuwa sansanin sake tarbiyar da su a Gombe

Mayakan ‘yan kungiyar Boko Haram 43 da suka mika wuya ga dakarun Operation Lafiya Dole makonni da suka gabata

Idan dai baku manta ba a farkon watan nan ne NAIJ.com ta kawo muku cewa fiye da mayakan ‘yan kungiyar Boko Haram 70 suka mika wuya ga sojojin na Operation Lafiya Dole a Arewa maso Gabashin kasar.

Boko Haram: An gabatar da mayankan Boko Haram 43 da suka mika wuya zuwa sansanin sake tarbiyar da su a Gombe

Mayakan a lokacin da suke shirin shiga jirgin sama zuwa Gombe

KU KARANTA: Boko Haram: Wasu mayakan kungiyar Boko Haram sun sake mika wuya ga dakarun Operation Lafiya Dole

Janar Attahiru ya kira sauran mayakan kungiyar da su yi watsi da gwagwarmaya ta’addanci su kuma bijirewa shugabancin kungiyar Boko Haram wanda suke rayuwa a cikin wadata da walwala, yayin da su kuma ke fama balayin yunwa a cikin daji.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.naij.com

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamna Ganduje ya koka game da naira biliyan 9 da gwamnatinsa ke kashewa wajen biyan albashi a kowane wata

Gwamnatin Kano tana kashe naira biliyan 9 wajen biyan albashi a kowace wata
NAIJ.com
Mailfire view pixel