Ba cin zaɓen 2019 bane a gabana, face sauke amanar da aka ɗaura min – Inji Gwamna El-Rufai

Ba cin zaɓen 2019 bane a gabana, face sauke amanar da aka ɗaura min – Inji Gwamna El-Rufai

- Gwamnan jihar Kaduna yace ba batun tazarce bane a gabansa

- El-Rufai yace babban burinsa ya inganta rayuwan mutanen jihar Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna ya sake baiwa jama’a musamman masu bibiyan al’amuran siyasar kasar nan mamaki, inda ya bayyana cewa shi fa baya tsoron faduwa zabe, don kuwa ba zaben bane ma a gabansa.

Gwamnan El-Rufai ya bayyana haka ne a ranar Talata 18 ga watan Yuli, yayin daya karbi bakoncin shugaban hukumar samar da cigaba a fadin Duniya na kasar Birtaniya, Debbi Palmer a gidan gwamnati.

KU KARANTA: So ko hauka? Tsananin soyayya ya jefa wata budurwa gidan yari, zaman wata 7 (KARANTA)

“Ba zan damu ba ko na fadi zaben 2019, ko kuwa na samu nasara, abinda na sanya a gaba kawai shine sauke nauyin dake kaina iya gwargwado.” Inji El-Rufai

Ba cin zaɓen 2019 bane a gabana, face sauke amanar da aka ɗaura min – Inji Gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai

Gwamnan ya kara da cewa “Duk wani gwamna na son yin abinda muke yi a jihar nan, amma saboda siyasa, yasa sun kasa daukan wadannan matakai. Ni kuwa ba haka nake ba, zan cigaba da yin abinda ya kamata, ko ba komai, yayanmu da jikokin mu zasu amfana.”

Ba cin zaɓen 2019 bane a gabana, face sauke amanar da aka ɗaura min – Inji Gwamna El-Rufai

Gwamna El-Rufai

NAIJ.com ta ruwaito akwai rade raden wai gwamnan na daya daga cikin wadanda ke sha’awar tsayawa takara karo na biyu a jihohinsu, sai dai lokaci ne kadai zai iya tabbatar da wannan jita jita.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Dan Najeriya yace gwamnati ta bashi umarnin yin sata, kalla:

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel