Yadda El-Rufai ya ki Buhari a 2010 amma yake yaba masa a 2017

Yadda El-Rufai ya ki Buhari a 2010 amma yake yaba masa a 2017

- Gwamnan jihar Kaduna ya bukaci shugaba Buhari ya bar siyasa a 2010

- Tsohon ministan na birnin tarayya ya bayyana Buhari a matsayin dan takara da bazai moru ba

- Amma a yanzu El-Rufai ya zamo daya daga cikin manyan magoya bayan Buhari

Sabanin sabon wakokin sa na yabo ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, a shekarar 2010 gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana Janar din waccen lokaci Muhammadu Buhari a matsayin dan takara da ba zai iya tabuka komai ba.

NAIJ.com ta tattaro cewa tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara a shafukan zumunta, Reno Omokri ne ya bayyana wasu jaridu a shafin san a Facebook inda El-Rufai ke sukar tsohon shugaban kasa, Ibrahim Babangida da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayinda ya bayyana su a matsayin yan takara da suka tashi daga aiki.

KU KARANTA KUMA: Ta sayar da jaririnta akan N700,000, an bata rabin buhun shinkafa a maimakon Kudin

A cewar jaridar Sun na ranar 20 ga watan Satumba, 201o, El-Rufai ya bukaci Babangida da Buhari da su janye takarar shugabancin kasa a 2011.

A halin yanzu, NAIJ.com ta rahoto cewa tsohon kakkakin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya bayyana shugaban kasa mai ci a matsayin ‘kuskure’.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200

Gwamnatin Katsina ta ƙara yawan kunshin jin dadi na NYSC da kashi 200
NAIJ.com
Mailfire view pixel