Wani Dan Najeriya na fuskantar barazanar dogon dauri a Kasar waje

Wani Dan Najeriya na fuskantar barazanar dogon dauri a Kasar waje

- Ana shirin daure wani mutumi 'Dan Najeriya a Kasar Amurka

- Kunle Sodipo na iya karewa a gidan yari idan ba a yi wasa ba

- Ana zargin wannan mutumi da laifin damfarar Amurka makudan daloli

Kwanan nan mu ka ji labarin cewa ana zargin wani mutumi Dan Najeriya Mista Kunle Sodipo Williams da laifin damfarar Hukumomin Kasar Amurka makudan daloli har Miliyan 12.

Wani Dan Najeriya na fuskantar barazanar dogon dauri a Kasar waje

Hoton Kunle Sodipo Williams daga Jaridar Vanguard

Wannan mutumi ya bayyana da bakin sa cewa ya aikata laifin da ake zargin sa da shi su na zamba har Dala Miliyan $12 da kuma rashin gaskiya a lokacin zabe da ma shiga Kasar Amurka ba tare da ka'ida ba.

KU KARANTA: Sarki Musulmi ya kai ziyarwa wajen babban Shehi

Wannan mutumi da ke zaune a Garin St. Louis na Birnin Missouri na fuskantar barazanar daurin shekaru 20 a gidan maza. Mista Kunle Sodipo mai shekaru 56 dai ya buga ta'adi iri-iri a Kasar Amurka.

A Najeriya kuwa Rundunar Sojin Najeriya ta damke wani Sojan karya kwanakin baya. Wannan abu ya faru ne a lokacin da Mukaddashin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zo Jihar Neja.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

An bude hanyar Nyanya da ke Birnin Tarayya

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel