Yadda Sojoji da yakin basasa suka yi sanadiyyar tabarbarewar Najeriya – Inji Atiku

Yadda Sojoji da yakin basasa suka yi sanadiyyar tabarbarewar Najeriya – Inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yakin basasan Najeriya na watanni 30 da aka kwashe ana fafatawa ne yayi sanadiyyar lalacewar daidaito a tsarin mulkin Najeriya.

Atiku ya bayyana haka ne a yayin taron kara ma juna sani akan hanyoyin tattaunawa da juna don samar da hadin kan kasa, inda yace sahihin sauyin tsarin mulkin kasa ne kadai hanya mafi tabbatar da ingantaccen mulki a Najeriya.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya kai ma Shehi Dahiru Bauchi ziyara (HOTUNA)

“Tsananin karfin gwamnatin tarayya tare da karyewar farashin mai da nuna halin ko in kula ga harkar sarrafa sauran ma’adanai ne ya janyo karyewar jihohi da dama.

Yadda Sojoji da yakin basasa suka yi sanadiyyar tabarbarewar Najeriya – Inji Atiku

Atiku

“Misali idan gwamnatin tarayya ta amshe kudaden da kasar ke samu, sai kuma ta raba su yadda kasonta yafi tsoka, wannan shine ya kawo mu a yau, inda muke samar da sabbin ma’aikatu a maimakon mu inganta wadanda suke kasa.” Inji Atiku.

Daga karshe Atiku ya bayyana babu laifi ga wasu mutane su nemi a yi gyaran tsarin mulkin kasa, “Bai kamata mu dinga muzanta masu bukatan ganin an sauya tsarin Najeriya ba, kamata yayi mu fahimci manufarsu, mu wanke musu hawaye.

“Sai dai ba zamu taba fahimtar hakan ba har sai mun zauna dasu mun saurari koke kokensu.” Inji Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, Turakin Adamawa, kamar yadda majiyar NAIJ.com, jaridar The Nation ta ruwaito.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel