Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

- Deborah Philipus, daya daga cikin matan da yan Boko Haram suka sace ta ce ‘yan ta’addan na kula da su sosai

- Wata mata da aka sace, Amina Adam Gomdia, ta bayyana cewa ita malama ce a makarantar kwalejin karantar da ilimin kiwon kifi na tarayya, Baga

- Matan sun roki gwamnatin tarayya da ta ceto su kamar yan matan Chibok

‘Yan ta’addan Boko Haram sun saki wani sabon bidiyo na wasu mata 10 da ‘yan ta’addan suka sace kwanan nan bayan wani hari da suka kai ga ayarin motocin ‘yan sanda a jihar Borno.

Sahara Reportaers wacce ta buga bidiyon ta bayyana cewa ‘yan ta’addan sun aiko da saki bidiyo mai tsawon mintuna 4 da sakan 41 a ranar Litinin, 17 ga watan Yuli.

Koda yake baza’a iya tabbatarwa ko dukkan matan ‘yan sanda bane ko matayen jami’an ‘yan sanda, an dai rahoto cewa an sace su ne bayan harin da ‘yan ta’addan suka kai ga wani jerin motocin ‘yan sanda dake tafiya zuwa Maiduguri a hanyar Damboa.

Matar da ta bayyana cewa mayakan na Boko Haram na kula da su saosai tun bayan sace sun ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta daina karyata sace sun da akayi.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun tsare wani dan jarida akan sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook

Ta kara da cewa daga lokacin da aka sace sun, ‘yan Boko Haram sun gyara masu raunukan su sannan kuma basu rasa komai ban a daga abinci da ruwa.

Wata mata cikin wadanda aka sacen, Amina Adam Gomdia, ta bayyana kanta a matsayin malama a makarantar Federal College of Fisheries, Baga.

Amina ta ce ta zamo bazawara ne tun bayan da Boko Haram suka kashe mijinta da ‘yaranta biyu a gaban idanunta a farkon lokacin da Boko Haram suka fara kai hari Maiduguri.

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci a labarin da Sahara Reporters suka wallafa

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

Daya daga cikin matan da aka sace a bidiyon da Sahara reporters suka wallafa

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci wanda Sahara Reporters suka wallafa

Boko Haram sun saki sabon bidiyo na mata 10 da suka sace daga ayarin motoci

Matan da aka saki sabon bidiyo wanda Sahara Reporters suka wallafa

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel