Shugabanin addinin musulunci sun yi Allah wadai da kalaman Danjuma da dattawan kirista

Shugabanin addinin musulunci sun yi Allah wadai da kalaman Danjuma da dattawan kirista

- Kungiyar Jama'atu Nasir Islam ta yi da zargin dattawan kirista na kasa

- Kungiyar ta ce zargin ajanda na musuluntar da Najeriya ba gaskiya ba ne

- Sakataren kungiyar ya ce kalaman wata hanyar karkatar da hankalin mutane daga kisan kiyashi da aka yiwa al’ummar musulmai a jiyar Taraba ne

Kungiyar Jama'atu Nasir Islam (JNI) ta yi watsi da kalaman janar T.Y Danjuma mai ritaya da kuma dan kungiyar dattawan kirista na kasa NCEF cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na kokarin musuluntar da Najeriya.

Idan dai baku manta ba a makon da ta gabata ne NAIJ.com ta kawo muku rahoto cewa kungiyar dattawan kirista na kasa sun zargi shugabanin addinin musulunci da wata ajanda na musuluntar da kasar Najeriya.

A lokacin da suka mai da martanin kan zargin, kungiyar addini musulunci a karkashin jagorancin sarkin musulmi sun yi Allah wadai da kalaman dattawan, kuma abin mamaki a ce kamar T.Y Danjuma da wasu shugabanin addinin kirista suka fito da irin wannan kalaman.

Shugabanin addinin musulunci sun yi Allah wadai da kalaman Danjuma da dattawan kirista

Mabiyar addinin Islama

Babban sakataren JNI, Dr. Aliyu Abubakar-Khalid, wanda ya yi magana da manema labarai a Kaduna a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli ya ce wannan wani hanyar karkatar da hankalin mutane daga kisan kiyashi da aka yiwa al’ummar musulmai a jiyar Taraba.

KU KARANTA: Sarkin Musulmi ya kai ma Shehi Dahiru Bauchi ziyara (HOTUNA)

Sakataren ya ci gaba da cewa irin wannan kalaman bai da ce da dattawan ba. Ya ce, in har akwai wani kirista da aka tilastawa ya yi ridda a kasar zai su fito su yi bayani.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose

Shiga APC kamar barin hanyar yesu almasihu ne ka bi hanyar shaidan - Fayose
NAIJ.com
Mailfire view pixel