Ta sayar da jaririnta akan N700,000, an bata rabin buhun shinkafa a maimakon Kudin

Ta sayar da jaririnta akan N700,000, an bata rabin buhun shinkafa a maimakon Kudin

Wata matashiya da aka amabatara da Chioma Fidelis mai shekaru 20 ta shiga hannun jami’an yan sanda bayan an kama ta da laifin yasar da ‘yar ta mai watanni biyu a duniya a kan kudi naira dubu dari bakwai.

A halin da ake ciki Fidelis wacce ta fito daga karamar hukumar Ehime na jihar Imo ta bayyana cewa bata amshi wadannan kudade da ake tuhumarta a kai ba.

Inda ta bayyana cewa a maimakon haka, an bata shinkafa rabin buhu, kayan masarufi, kujeru da kuma buhuhunan simitin wanda tayi amfani da shi gurin gyara gidanta.

An kama Fidelis ne tare da wasu mutane 40 da suka aikata laifuka iri daban-daban.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Chris Ezike, ya ce sun damke masu safarar yaran ne a ranar 10 ga watan Yuli bayan an sun samu rahoto a kan afkuwar al’amarin.

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun tsare wani dan jarida akan sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook

Da take sanar wa ‘yan sanda yadda alamarin yaafku, Fidelis ta ce dama ta haihu ne a bisa kuskure ba tare da ta shirya zama uwa ba, kuma daga bisani ta kasa kulawa da jaririn, wanda hakan ne ya sa ta yanke hukuncin siyar da shi.

‘Yan sandan sun kuma kama Misis Chidimma Unakala Mgba, mai shekaru 34 wacce ita ta gudanar da cinikayyar, inda ita kuwa ta fadawa ‘yan sandan cewa ta aikata laifin ne saboda ta ga cewa uwar dan ba za ta iya kulawa da shi ba. Hasali ma a lokacin da ta dauki yaran, ya na fama da matsananciyar yunwa, cewar ta.

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel