Talauci da yunwa ne ke janyo tarzoma da tashin hankulla a Najeriya - Peter Obi

Talauci da yunwa ne ke janyo tarzoma da tashin hankulla a Najeriya - Peter Obi

- Tsohon gwamnan Jihar Anambra, Mr Peter Obi, ya tantance cewa yunwa da talauci ne ja gaba daga cikin dalilan da ke haifar da tarzomar raba Najeriya daga mafiya yawan kabilun kasar

- Wadannan yanayi guda biyu suna tilasta yan kasar neman dauki ta kowacca hanya, a yayinda wasu kuma ke amfani da kabilanci gurin kore wannan damuwar daga kansu

Obi yayi wadannan jawaban ne a wani taro a birnin kalaba da aka wa suna da 7th edition of the Bridge Leadership Foundation, wanda daya daga tsofaffin gwamnan jihar Senator Liyel Imoke ya shirya Taken taron kuwa shine- Made in Nigeria- Local production, global market.

Obi, a wani bangaren jawabinsa da yayi a karkashin unwanin shugabanci da amana, yayi tsokaci da nuni cewa rashin hangen nesan wasu daga shuwagabannin kasar ne ya ke haifar da rikice-rikicen kabilanci a kasar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa ya bada misalai da dama; daga ciki akwai boko Haram a Arewa maso gabashin kasar,yan ta'addan yankin nija delta,yan tada kayar bayafara a kudu maso gabashin kasar, da rikice-rikicen fulani da jama'a. Ya nuna cewa duk wadannan sun auku ne sakamakon rashin kyautatuwan shugabanci.

Talauci da yunwa ne ke janyo tarzoma da tashin hankulla a Najeriya - Peter Obi

Tsohon gwamnan Jihar Anambra Peter Obi

Obi ya kara da cewa Najeria nada isassun ma'adanai da ma'aikatanda ka iya cigabantar da kasar ta kai matsayin kasa mafi daukaka a duniya, amma rashin hangen nesan shuwagabanni ke dakularda kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya zata hana yin finafinai, da wake-waken gida a kasan waje

A karshen jawabinsa ya yabawa Imoke a cigabantarda wannan tsari da ya dauko na taron da sukayi har tsawon shekaru bakwai tareda nuna cewa gina matasa shine gina Al'ummar jiha da kasa baki daya.

ku biyomu a facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa/

ko a twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon tarzomar mutane a jihar kano

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Aisha Buhari zata karbi baƙoncin Buhari, Osinbajo tare da Ministocin Najeriya a ofishinta

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel