Kano: Wani jigon jam’iyyar APC ya jinjinawa gwamna Ganduje

Kano: Wani jigon jam’iyyar APC ya jinjinawa gwamna Ganduje

- Tinubu ya jinjinwa gwamnan jihar Kano kan ayyukan na ciyar da jihar gaba

- Tinubu ya ziyarci Kano domin gaisuwar ta'aziyyar rasuwar marigayi Danmasanin Kano

- Jigon jam’iyyar APC ya bukaci al’ummar jihar da su ba gwamnasu goyon baya

Jigon jam’iyyar mai mulki ta APC, sanata Bola Ahmed Tinubu ya yaba aikace-aikacen gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Tinubu ya yi wannan yabon ne a lokacin wani ta'aziyyar sa kan rasuwar marigayi Danmasanin Kano, Dr. Yusuf Maitama Sule, a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli a Kano.

Tinubu ya ce: " Mun yaba kokarin ka kuma kana damuwa ta yanda zaka inganta rayuwar al’ummar jihar Kano. Ka yi abubuwa da dama domin ka ciyar da jihar gaba”.

Kano: Wani jigon jam’iyyar APC ya jinjinawa gwamna Ganduje

Jigon jam’iyyar mai mulki ta APC, sanata Bola Ahmed Tinubu

NAIJ.com ta ruwaito cewa, Tinubu ya yi kira ga al'ummar jihar Kano baki daya da su ci gaba da ba gwamnan goyon baya a kowane lokaci domin ci gaban jihar.

KU KARANTA: Ýar kunar bakin wake ta hallaka masu bauta 10 a masallacin Maiduguri

"Kano wata jihar ne mai muhimmanci ga tattalin arzikin kasar. Za a iya kirkiro da ayyukan yi ga matasan jihar da yawan mutanen da Allah ya albarkaci jihar Kano”. A cewar jigon dan siyasan.

A nasa jawabi, gwamna Ganduje ya gode ga ziyarar Bola Tinubu inda ya bayyana Tunibu a matsayin wani jigon kuma mai basira na siyasa a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel