Siyasa: APC ta tofa albarkacin bakin ta kan kiranyen shugaban majalisar dattawa

Siyasa: APC ta tofa albarkacin bakin ta kan kiranyen shugaban majalisar dattawa

- Mazabar sanata Saraki ta nisanci kanta daga kiran a dawo da shugaban majalisar dattawan Najeriya

- Shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar Ilorin ta yamma ya ce jam’iyyar ba ta san da masu wannan kiran ba

- Jam’iyyar APC ta hada taron addu’a na musamman domin a yiwa Saraki addu’a

Jama'iyyar mai mulki ta APC a karamar hukumar llorin ta yamma a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli ta nisanta kanta daga waɗanda su ke kira ga kiranyen shugaban majalisar dattawa, Dr. Bukola Saraki daga majalisar dattijai.

Alhaji Suleiman Bala, shugaban jam’iyyar APC a karamar hukumar llorin ta yamma ya shaida wa manema labarai a Ilorin fadar gwamnatin jihar Kwara cewa jam’yyara ba ta san da kungiyar da kuma 'yan kungiyar da suke ikirarin dawo da shugaban majalisar.

NAIJ.com ta ruwaito cewa shugaban jam’iyyar ya yi wannan magana ne a wani taron addu’a na musamman wanda aka shirya don girmamawa Saraki.

Siyasa: APC ta tofa albarkacin bakin ta kan kiranyen shugaban majalisar dattawa

Sanata Bukola Saraki a lokacin da yake rantswa a matsayin shugaban majalisar dattawa

Ya ce: “ Waɗanda su ke kira da a dawo da shugaban mu kuma shugaban majalisar dattawa, ba mu san da su ba kuma ba ‘yan asalin jihar ba ne”.

KU KARANTA: Ka-ka-kara-kaka: Gwamnatin Tarayya ta shiga Kotu da 'Yan Majalisa

Shugaban ya ci gaba da cewa an shirya taron addua’a na musamman ne domin a nema wa Saraki kariya daga Allah a kowane lokaci.

Cikin wadanda suka halarci taron addu’an sun hada da jami’an jam’iyyar APC daga karamar hukumar da kuma jihar baki daya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara

An tsinci gawar dan jaridar da ya bata a jihar Anambara
NAIJ.com
Mailfire view pixel