NEJA: Gwamnatin jihar Neja za ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da miliyan 30

NEJA: Gwamnatin jihar Neja za ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da miliyan 30

- Gwamnatin jihar Neja za ta tallafa wa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa miliyan 30 a jihar

- Bello ya bukaci mazaunan yanki da su kaurace daga hanyoyin ruwa domin su kare kansu daga ambaliyar ruwa

- Gwamna Bello ya yi ta'aziyyar ga Malam Saad Abdullahi, wani mazaunin yankin Checheniya wanda ya rasa matansa 2 da yara 6 ga ambaliyar ruwan

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello ya amince da kudi naira miliyan 30 ga hukumar bada agaji na gaggawa ta jihar (NSEMA) don samar da kayan agaji ga wadanda ke fama da ambaliyar ruwa a Suleja.

A sanarwar babban sakataren labarai na gwamna, Malam Jibrin Ndace a Minna a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli ya ce gwaman Bello ya amince da tallafin ne a lokacin da ya ziyarci wasu wuraren da ambaliyar ruwar ta shafa a cikin yankunan kananan hukumomin Suleja da Lapai na jihar.

Idan dai baku manta ba NAIJ.com ta kawo muku rahoto cewa mutane 11 suka rasa rayukansu inda kuma gidaje da dama suka halaka a lokacin da ambaliyar ruwar ta barke a ranar 8 ga watan Yuli a Suleja.

NEJA: Gwamnatin jihar Neja za ta tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da miliyan 30

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Bello

A makon da ta gabata ne kuma mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya umurni ministar kudi, Kemi Adeosun da ta gaggauta fitar da naira biliyan 1.6 daga babban bankin kasar, CBN ta rabawa jihohi 15 da ambaliyar ruwa na kwananna na ta shafa.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya aika sako ga mutanen Jihar Sokoto

Gwamnan ya bukaci mazaunan yanki da su kaurace daga hanyoyin ruwa domin su kare kansu daga ambaliyar ruwa.

Ndace ya ce gwamnan ya yi ta'aziyyar ga Malam Saad Abdullahi, wani mazaunin yankin Checheniya wanda ya rasa matansa 2 da yara 6 ga ambaliyar ruwan.

Ndace ya ci gaba da cewa gwamna Bello ya kuma ziyarci kauyen Sabo Orehi a karamar hukumar Lapai inda gadar da ta hade jihar da Kogi ta rushe saboda yawan ruwan sama.

Bello ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta gina wata sabon gada nan da kwanaki 40.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?

Taron Majalisar zartarwa na yau zai gudana a Ofishin Uwargidar shugaban kasa, shin menene dalili?
NAIJ.com
Mailfire view pixel